KADRA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara aikin sakewa gadar kawo zani

KADRA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara aikin sakewa gadar kawo zani

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara aikin tuge wani bangare na gadar nan ta Kawo inda ake shirin kara mata karfi kamar yadda gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta yi alkawari tun a bara.

Kawo yanzu wannan aiki ya fara kankama gadan-gadan domin ma’aikata sun soma ruguza wannan gada. Hukumar KADRA mai alhakin gyaran titunan Kaduna ta bayyana wannan.

Hukumar KADRA ta ce ta samar da wasu hanyoyi na dabam da jama’a za su rika bi yayin da ake aiki a wannan gada. A halin yanzu babu abin hawar da ke iya bi ta saman gadar ta Kawo.

Shugaban hukumar KADRA, Injiniya Mohammed Lawal Magaji ya yi kira ga jama’a su yi hakuri da matsatsin da aka jefa su a sakamakon wannan aiki da gwamnatin Kaduna ta baro.

Mohammed Lawal Magaji ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a ranar Talata. Lawal Magaji ya ce sun samar da hanyoyi da duk masu abin hawa za su koma bi.

KU KARANTA: An hana wata katuwar mota da ta fito daga Legas shiga Jihar Neja

KADRA ta ce: “An kirkiri hanyoyi uku a Gari; an warewa manyan motoci da gingimari da tankoki hanyoyi biyu ta waje, inda aka bar hanyar ciki domin sauran masu abubuwan hawa.”

Magaji ya ce: “Masu shigowa Kaduna daga Zariya su na da sahun hanyoyi hudu, hanyoyi biyu sun yi cikin Gari, sai kuma sauran hanyoyin su ka bi ta babban titi da kuma Mando.”

Shugaban hukumar ya kara cewa: “Hanyar Mando ta na da sahu biyu wanda su ka bi titin Ali Akilu, amma za su tike a hanyar shiga Cocin St Patrick, kafin a koma babbar hanya.”

Yanzu haka an komawa bin wadannan hanyoyi kamar yadda KADRA ta bayyana a shafinta na Tuwita. An ga hotuna da kuma bidiyon wasu ma’aikata su na banbare saman gadar.

Jami’an gwamnati da masu duba wannan kwangila su na bakin aiki a daidai lokacin da gwamnati ta umarci jama’a su zauna a cikin gida domin takaita yaduwar Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel