Masu bilicin na cikin hatsarin kamuwa da cutar coronavirus - Kwararren likita

Masu bilicin na cikin hatsarin kamuwa da cutar coronavirus - Kwararren likita

Wani kwararren likita, Dr Chinonso Egemba, ya ce masu amfani da man kara hasken fata, ka iya fadawa halin rashin lafiya mai tsanani ko ma su mutu sanadiyar cutar coronavirus.

Egemba, ya fada ma kanfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba, cewa wasu mayun bilicin da sabulu na dauke da sinadarin ‘steroids’, wanda ke rage karfin kariyar da jiki ke dashi.

Ya bayyana garkuwar jiki, a matsayin kariyar da jiki ke dashi wajen yakar kwayoyin cututtuka da ke haifar da coronavirus da sauran kwayoyin halitta da ke taba jikin dan Adam, da wanda yake shaka a kullun.

“Idan kana bilicin, toh ka daina saboda yana rage garkuwar jiki sannan kuma mutane ko marasa lafiya da ke da karancin garkuwar jiki sun fi jin jiki kuma suna iya mutuwa sakamakon cutar.

“Sinadarin ‘steroids’ su kan kasance magunguna masu hana kumburi, kuma kumburi na daya daga cikin hanyoyin da jikinmu ke zubar da bakin abubuwa. Yana iya kasancewa ta kumburin jiki ko kuma ta marurai ko jajjayen kuraje a jiki.

Ma su bilicin na cikin hatsarin kamuwa da cutar coronavirus - Kwararrun likitoci
Ma su bilicin na cikin hatsarin kamuwa da cutar coronavirus - Kwararrun likitoci
Asali: UGC

“Don haka sinadarin “steroids” na rage wa jiki karfi daga duk wani abu da ka iya haddasa kumburi.”

“A yanzu akwai na’i daban-daban na mayuka da sabulan bilicin amma wasu na dauke da “steroids” kuma yana iya haska fatar jiki.”

“Idan mutum ya yi amfani da irin wannan mai ko sabulun na tsawon lokaci, jikinsa zai shanye sinadarin da ke cikin man sannan sai ya rage masa karfin garkuwar jikinsa,” in ji shi.

Egemba ya ce wasu kwararru a fannin fata marasa lasisi na baiwa abokan harkarsu sinadarin’steriods’, a matsayin kwayar magani da sunan zai taimaka masu wajen haskaka fatar jikinsu.

“Idan mutum ya hadiyi wannan kwayar magani, toh yana raunata garkuwar jikinsa ne.

“Don haka ta bangaren COVID-19, kasancewa da garkuwar jiki mai karfi na daya daga cikin manyan hanyoyin waraka daga cutar sannan idan garkuwar jiki bai da karfi sakamakon bilicin, mutum zai fi jin jiki koma ya mutu ta sanadiyar cutar coronavirus,” in ji shi.

Ya bukaci yan Najeriya da su riki tsari mai inganta lafiya domin bunkasa garkuwar jikinsu.

“Ku daina shan sigari, a sha giya kadan koma a bari kwata-kwata, ayi bacci da kyau, a ci abinci mai gina jiki, a sha kayan marmari da gayayyaki, a dunga motsa jiki da rage wahalar da jiki.

“Wannan na taimakawa wajen bunkasa garkuwar jiki a kokarin yakar coronavirus,” in ji Egemba.

KU KARANTA KUMA: An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

A gefe daya mun ji cewa an sallami masu cutar Coronavirus shida da sukayi jinya a jihar Osun bayan gwaji biyu daban-daban ya nuna cewa sun warke daga cutar.

Gwamnan jihar, Gboyega Oyetola, ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel