Gwamnan Nasarawa ya siya wa yan majalisa motocin alfarma guda 24

Gwamnan Nasarawa ya siya wa yan majalisa motocin alfarma guda 24

Kakakin majalisar dokokin jahar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi, a ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu, ya ce gwamnan jahar, Abdullahi Sule, ya ba yan majalisar dokokin jahar su 24 motocin Toyota Hilux guda 24.

Abdullahi ya ce wannan karamci na gwamnan zai kawo ci gaba sosai wajen aiwatar da ayyukan bangaren dokoki, musamman ta fannin rangajin gani da ido.

A cewarsa, “al’ada ce a kowace majalisar dokoki, gwamnatin jaha kan siya wa zababbun mambobin majalisar motocin aiki.

“Hakan ya kasance domin ba yan majalisar damar aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyansu yanda ya kamata.

“Kamar yadda kuke gani, an siyi sabbin motocin Hilux wanda zai ba mambobin majalisar damar shiga kowani lungu da sako na mazabunsu.”

Gwamnan Nasarawa ya siya wa yan majalisa motocin alfarma guda 24
Gwamnan Nasarawa ya siya wa yan majalisa motocin alfarma guda 24
Asali: UGC

Ya ba gwamnatin jahar tabbacin samun goyon bayansu ta bangaren aiki domin tabbatar da ganin ci gaba a fadin jahar.

Kakakin majalisar ya yi kira ga mutanen jahar da su ba yan majalisar da bangaren zartarwa goyon baya, domin su cimma nasara ta yadda za su ci moriyar damokradiyya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke yaki da annobar coronavirus.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Karin mutane biyar sun kamu da coronavirus a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya bayar da umarnin dakatar da cire wani kasafi daga cikin albashin ma'aikata a jihar.

Bala Muhammad a gaggauce ya umarci babban akantan jihar da kuma masu ruwa da tsaki kan dakatar da tatsar albashin ma'aikatan jihar a matsayin gudunmuwarsu ta yakar cutar Korona.

Gwamnan ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin, 14 ga Afrilun 2020 yayin kaddamar da kwamitin habaka tattalin arzikin jihar a wannan yanayi na annobar cutar Korona.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, gwamnan yace wannan sabon hukunci ya biyo bayan korafen-korafen da wani rukuni na ma'aikatan jihar suka shigar.

A ranar Juma'a 3, ga Afrilun 2020, majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta yanke hukuncin cire wani kasafi daga albashin ma'aikatan jihar na watannin Afrilu, Mayu da kuma Yuni.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel