Gwamnan Kaduna ya ce a yafewa wasu masu laifi da ke daure a gidan yari

Gwamnan Kaduna ya ce a yafewa wasu masu laifi da ke daure a gidan yari

Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki wani mataki na musamman domin rage yaduwar cutar Corornavirus. Gwamna Nasir El-Rufai ya amince a saki wasu da ke tsare a gidan yari.

A ranar Talata 14 ga watan Afrilu, 2020, Channels TV ta rahoto gwamnan Kaduna ya na bada umarnin fito da wasu masu laifi 72 da ke daure a gidajen yarin Kaduna da Kafanchan.

Kwamishinar shari’a kuma babbar lauyar gwamnatin Kaduna, Aisha Dikko, ta sanar da hakan, inda ta bayyana cewa har an saki wadannan mutane kamar yadda aka bada umarnin.

Dikko ta ce sun saki mutane 69 daga gidan yarin da ke garin Kaduna yayin da aka fito da wasu Bayin Allah uku da ke daure a dayan gidan kurkukun jihar da ke cikin Garin Kafanchan.

Da ta ke bayanin yadda aka sallami wadannan mutane da ke daure, ta bayyana cewa 42 daga cikin wadanda aka fitar daga kurkukun Kaduna sun biya tarar da ba ta wuce N50, 000 ba.

KU KARANTA: Bello El-Rufai zai kai ‘Dan Jarida kotu saboda rahoton fyade

Gwamnan Kaduna ya ce a yafewa wasu masu laifi da ke daure a gidan yari
Gwamnan Kaduna ya ce a yafewa wasu masu laifi da ke daure a gidan yari
Asali: Facebook

Kwamishinar shari’ar ta ce an kuma sallami wasu mutum uku daban da watanni kusan shida rak su ka rage masu daga cikin daurin shekaru akalla uku da Alkali ya yanke masu a kotu.

Daya daga cikin wadanda aka sallama ya shafe 75% na zaman kason da aka yanke masa. Haka zalika daga ciki akwai sauran mutane 22 masu kananan laifuffuka da aka ce su tafi gida.

A bayanin Kwamishinar an ji cewa akwai wani Dattijo da gwamnati ta sallama daga kurkuku a sakamakon la’akari da aka yi da yawan shekarunsa, a dalilin haka aka yi masa afuwa.

Gwamnatin El-Rufai ta yi wannan yunkuri ne domin ta rage cunkuso a cikin gidajen yarin da ke fadin jihar. Wannan mataki zai taimaka wajen rage yiwuwar yaduwar cutar COVID-19.

A jihar Osun kuma mun ji cewa Jami’ai sun kama Kansilan na Mazabar Odo Otin da ya dade ya na sukar mai girma gwamna Gboyega Oyetola ta shafin Facebook da ya bude da wani suna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel