Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta sallami mutum 1 da ya warke

Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta sallami mutum 1 da ya warke

- An sallami mutum daya cikin marasa lafiya shida da suka kamu da cutar COVID-19 a jahar Kaduna

- Kwamishinar lafiya ta jahar, Dr Amina Mohammed Baloni ce ta sanar da hakan, ta ce mara lafiyan ya warke

- Ta ce an sallami mutumin ne bayan karo na biyu da aka yi masa gwajin cutar a ranar Talata, wanda sakamakonsa ya nuna ya warke daga cutar

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana cewa ta sallami mutum daya cikin marasa lafiya shida da suka kamu da cutar COVID-19, daga cibiyar kula da wadanda suka kamu.

Kwamishinar lafiya ta jahar, Dr Amina Mohammed Baloni wacce ta sanar da labarin a ranar Laraba, ta bayyana cewa mara lafiyan ya warke bayan kula da ya samu a cibiyar killace masu cutar.

Ta ce an sallami mutumin ne bayan karo na biyu da aka yi masa gwajin cutar a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, wanda sakamakonsa ya nuna ya warke daga cutar.

Kwamishinar ta ci gaba da cewa: “gwamnatin jahar na duba izuwa ga warkewar sauran mutane biyar da suka kamu a jahar.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Karin mutane biyar sun kamu da coronavirus a Kano

Dr Baloni ta yaba da jajircewar da kungiyoyi daba-daban wajen bayar da gudunmawa a kokarin da ake na dakile annobar ta COVID-19.

Ta ce: “Muna kuma mika jinjina ga kwararrun likitocin da ke aiki a cibiyar kula da cutar kan nasarar da suka samu wajen warkar da wannan mara lafiya.

“Ma’aikatar lafiya na tunatar da mazauna jahar Kaduna cewa, ya fi alkhairi da sauki mutum ya kula da matakan kare kai fiye da warkar da COVID-19. Ya zama dole mutane su lazumci wanke hannayensu da sabulu da ruwa akai-akai da kuma nisantan taron jama’a.

“Ana kuma shawartarsu da su guji taron mutane da yawa sannan su zauna a gida, sai dai idan ya zama dole su fita. A duk inda suke, su kula da tsafta."

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta dauki wani mataki na musamman domin rage yaduwar cutar Corornavirus. Gwamna Nasir El-Rufai ya amince a saki wasu da ke tsare a gidan yari.

A ranar Talata 14 ga watan Afrilu, 2020, Channels TV ta rahoto gwamnan Kaduna ya na bada umarnin fito da wasu masu laifi 72 da ke daure a gidajen yarin Kaduna da Kafanchan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel