Annobar Coronavirus: Sakamakon gwajin da aka yi ma wasu mutane 22 a Gombe ya fito

Annobar Coronavirus: Sakamakon gwajin da aka yi ma wasu mutane 22 a Gombe ya fito

Gwamnatin jahar Gombe, ta ce sakamakon gwajin mutane 22 da ake zargin suna da coronavirus, wanda aka aika cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya (NCDC) Abuja domin yi masu gwaji ya fito.

Sakamakon ya kuma nuna basa dauke da kwayar cutar ta COVID-19.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a jiya Talata, 14 ga watan Afrilu, a wani jawabin kai tsaye ga mutanen jahar.

Ya ce wata tawaga na musamman kan coronavirus karkashin jagorancin Farfesa Idris Mohammed sun gano wasu mutane 22 da ake zargin suna da ita sannan suka tura samfurinsu domin gwaji.

Inda aka dawo da sakamako wanda ya nuna basu da cutar.

Annobar Coronavirus: Sakamakon gwajin da aka yi ma wasu mutane 22 a Gombe ya fito
Annobar Coronavirus: Sakamakon gwajin da aka yi ma wasu mutane 22 a Gombe ya fito
Asali: UGC

Gwamnan ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa matakan magance lamarin da aka dauka na tasiri, sannan ya bukaci mazauna jahar da su ba gwamnati goyon baya a kokarinta na hana yaduwar cutar a jahar.

Ya kara da cewar yayinda ake kokarin bin dokar hana zirga-zirga da rufe iyakokin jahar, an zargi wasu mutane da hukumomin tsaro na taimakawa masu mota wajen shiga jahar a sace.

KU KARANTA KUMA: Annobar Coronavirus: Saudiyya ta baiwa mutane 1,676 marasa galihu tallafi a Kaduna da Kebbi

A gefe daya, ganin yadda azumi ya gabato a lokacin da ake fama da annobar Coronavirus, ‘Dan majalisar tarayya, Hon. Mohammed Umar Bago zai rabawa mutanensa tulin kayan abinci.

Honarabul Mohammed Umar Bago mai wakiltar Mazabar Chachaga a majalisar wakilan tarayya zai ba ‘Yan Mazabarsa kyautar manyan motoci har 11 cike da buhunan shinkafa.

Mohammed Bago ya bayyana cewa zai yi wannan ne domin fitar da mutane daga radadin wahalar da su ke ciki ganin an hana kowa fita a jihar Neja, sannan ga azumi ya gabato.

Bago ya ce babban Hadiminsa, Alhaji Abdulakeem Abdulrahman Oshinuga zai raba kayan. ‘Dan majalisar ya bayyana wannan ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook jiya.

Kowace gunduma za ta samu mota guda cike da buhun shinkafa inji ‘Dan majalisar. Abdulakeem Abdulrahman Oshinuga zai dauki alhakin raba abincin ga duk Mabukatan yankin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel