Annobar Coronavirus: Saudiyya ta baiwa mutane 1,676 marasa galihu tallafi a Kaduna da Kebbi

Annobar Coronavirus: Saudiyya ta baiwa mutane 1,676 marasa galihu tallafi a Kaduna da Kebbi

Gwamnatin kasar Saudiyya ta bayar da tallafin kayan abinci ga mutane 1000 a jahar Kaduna don rage musu radadin mawuyacin halin da suke ciki sanadiyyar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito Saudiyya ta bayar da tallafin ne ta hannun kungiyar Musulunci ta Duniya, tallafin ya hada ne da shinkafa, taliyar turawa da kuma man gyada.

KU KARANTA: Gwamnatin Legas ta gano sabbin mutane 119 dake dauke da alamomin COVID-19

An zabo mutanen ne daga unguwannin talakawa a Kaduna, kuma tsarin rabon ya nuna duk mutum ya samu buhun shinkafa kilo 1, katan na taliyar spaghetti da kuma man gyada lita 4.

Kwamishiniyar kula da jin dadi da walwalar jama’an jahar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ce ta jagoranci raba kayan, inda ta yi kira ga wadanda suka amfana da su ririta abin da suka samu.

Annobar Coronavirus: Saudiyya ta baiwa mutane 1,676 marasa galihu tallafi a Kaduna da Kebbi
Annobar Coronavirus: Saudiyya ta baiwa mutane 1,676 marasa galihu tallafi a Kaduna da Kebbi
Asali: UGC

Shi ma a nasa jawabin, jami’in kiwon lafiya na kungiyar, Muhammad Ahmad yace:

“Kungiyarmu za ta kashe riyal miliyan 1 a jahohin Arewa guda 7, amma mun zo Kaduna ne don raba abinci ga talakawa tare da kayan kariyar fuska da tabarau ga ma’aikatar kiwon lafiya ta Kaduna.”

Haka zalika kungiyar ta yi rabon kayan abinci ga mutane 676 a jahar Kebbi, wanda ta bi tsari wajen zabosu domin tabbatar da sun cika sharuddan kasancewa talakawa marasa karfi.

An zabo wadanda suka amfana da tallafin ne daga garuruwan Aliero, Argungu, Augie, Birnin Kebbi, Bunza, Kalgo, Gwandu, Jega da karamar hukumar Arewa.

Daga cikin kayan da kungiyar ta bayar akwai buhunan shinkafa kilo goma guda 676, katan 676 na taliya da man gyada, Inji jami’in kungiyar Sheikh Sharafudeen Sulaiman ya bayyana.

Sheikh Sulaiman yace wannan tallafi wani gudunmuwa ne daga kasar Saudiyya domin rage ma Musulmai radadin halin da annobar Coronavirus ta tsundumasu a ciki.

A jawabinsa, shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jahar Kebbi, Jafaru Muhammad ya gode ma kungiyar bisa tallafin abinci da kayan kariya da ta baiwa jahar.

Kungiyar Muslim World League ta yi alkawarin bayar da irin wannan tallafi a jahohin Borno, Bauchi, Jigawa Sakkwato da kuma Zamfara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng