Coronavirus za ta sa tattalin arzikin Najeriya ya tsuke da – 3.4%, Inji IMF

Coronavirus za ta sa tattalin arzikin Najeriya ya tsuke da – 3.4%, Inji IMF

Ganin yadda annobar COVID-19 ta ke yi wa tattalin arzikin kasashe ta’adi, cibiyar bada lamuni na Duniya IMF ta yi hasashen makomar tattalin Najeriya a wannan shekara.

Hukumar IMF ta na ganin cewa tattalin arzikin Najeriya zai gurgunce har ya tsuke da kashi -3.4% a wannan shekara ta 2020 a sakamakon annobar cutar nan ta Coronavirus.

IMF ta ce Najeriya za ta samu kanta cikin matsin lambar tattalin arzikin da ba ta taba ganin irinsa ba cikin shekaru 30 da su ka wuce, kuma karo na biyu a cikin shekaru biyar.

A cewar cibiyar IMF, halin da za a shiga a bana zai yi kama da abin da ya faru a 1987 da 1991 lokacin da tattalin arzikin Najeriya ya tsuke da kashi -10.87% da kuma -0.6%.

IMF ta fitar da wannan bayani ne a wani rahoto da ta fitar game da halin tattalin arzikin kasashen Duniya. An fitar da wannan rahoto ne a birnin Washington na kasar Amurka.

KU KARANTA: Coronavirus: Najeriya ta samu tallafin kayan asibiti daga UN

Babbar masaniyar tattalin arzikin IMF, Gita Gopinath, ta ce wannan matsin lamba da Duniya za ta shiga, shi ne mafi muni da za a fuskanta tun wanda aka yi fama da shi a 1929.

IMF ta koma yin taro ne ba tare da an halarci ofis ba saboda gudun yaduwar cutar COVID-19. Gita Gopinath ita ce shugabar sashen bincike da nazari na hukumar a halin yanzu.

Tsakanin shekarar 1929 zuwa 1932, tattalin arzikin Duniya ya tsuke da 16%. Hasashen da hukumar bada lamunin ta yi, ya nuna abubuwa za su dawo daidai a shekara mai zuwa.

Idan har hasashen IMF ya zama daidai, tattalin arzikin kasashen Duniya zai motsa da kashi 2.4% a 2021. A bana kasashen da su ka cigaba da masu tasowa duk sun shiga matsala.

Sin ce kadai ake tunani tattalinta ba zai wargaje kamar sauran kasashe ba. Hukumar ta yi nazari a kan kasashen Duniya 170. Najeriya ta na cikin kasar da samun arzikinta zai ragu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng