UN ta aikowa Gwamnatin Najeriya na’urorin taimakawa numfashi 50 ta filin jirgin NAII

UN ta aikowa Gwamnatin Najeriya na’urorin taimakawa numfashi 50 ta filin jirgin NAII

A Ranar Talata, 14 ga Watan Afrilu, gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbi wasu kayan asibiti da majalisar dinkin Duniya ta aiko da su kasar domin yakar annobar cutar COVID-19.

Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika da wasu daga cikin ‘Yan kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar COVID-19 a Najeriya ne su ka karbi wadannan tarin kaya.

Jaridar Punch ta rahoto cewa jami’an gwamnatin sun karbi wadannan kaya ne a babban filin tashi da saukar jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya na Abuja.

Hadi Sirika ya tabbatar da cewa wadannan kaya sun shigo hannunsu a shafinsa na Tuwita. Ministan ya yabawa majalisar da kamfanin jirgin da su ka taimaka da jigilar na’urorin.

Daga cikin wadannan kayan asibiti da aka kawo akwai na’urorin taimakawa numfashi watau ‘Ventilators’ na samfurin A30 50 da kuma wasu rigunan kare-kai na Malaman asibiti.

KU KARANTA: Gwamnati ta tabbatar da mutuwar wani Dattijo a sanadiyyar COVID-19

A kan yi amfani da na’urar Ventilators ne ga wadanda su ka kamu da cutar COVID-19 kuma har ta kai ta fara taba huhunsu, wanda hakan ke jawo maras lafiya ya gaza numfashi sosai.

Jaridar ta ce ana sa ran wadannan kaya da aka fara aikowa Najeriya somin-tabi ne na gudumuwar da majalisar dinkin Duniya za ta bada domin takaita yaduwar COVID-19.

Babban jami’in majalisar UN da ke Najeriya, Mista Edward Kallon ya bayyana cewa an sayo wadannan na’urori da kayan aiki ne daga wata gidauniya da aka kafa dalilin annobar.

Edward Kallon ya bayyana cewa a cikin wannan Watan za a sake aikowa Najeriya gudumuwar wasu kayan. Rahoton ya ce kayan sun iso jiya ne da kimanin karfe 5:00 na yamma.

Ministan harkar kiwon lafiyan Najeriya, Dr. Osagie Ehanire ya na cikin tawagar da ta karbi gudumuwar. Wannan zai taimakawa gwamnati wajen shawo kan cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel