Kaduna ta sassauta dokar hana fita na kwana biyu domin mutane su siya kayan abinci

Kaduna ta sassauta dokar hana fita na kwana biyu domin mutane su siya kayan abinci

Gwamnatin jahar Kaduna ta sassauta dokar hana walwala da ta sanya a fadin jahar, sakamakon annobar COVID-19.

Hakan zai kama daga ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, zuwa ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, ya bayyana cewa an sassauta dokar hana zirga-zirgan na kwanaki biyu ne.

Domin mutane su samu damar siyan kayayyakin abincin da za su ajiye a gidajensu da sauran kayayyakin amfani kafin a ci gaba da dokar hana fitan a ranar Alhamis.

Ya kara da cewar shagunan siyar da abinci da magunguna ne kadai aka ba izinin bude shagunansu daga karfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a wadannan ranaku.

Kaduna ta sassauta dokar hana fita na kwana biyu domin mutane su siya kayan abinci
Kaduna ta sassauta dokar hana fita na kwana biyu domin mutane su siya kayan abinci
Asali: UGC

A cewarsa, hakan na daga cikin manufar da aka amince dashi na sassauta dokar hana fita na kwanaki biyu a kowani mako, domin ba al’umma damar siyan abubuwan amfani da suka kare.

Gwamnatin jahar ta kuma shawarci mazauna jahar da su nisanci taron jama’a a yayinda suka je siyayya, sannan kuma cewa motocin haya su bi dokar mutum biyu a kowani layin mota.

A yayinda suke martani ga umurnin gwamnati, mazauna garin Kaduna sun yi korafin cewa suna wahala saboda rashin kudin siyan kayan abinci.

Sun bukaci gwamnatin da ta tallafa masu da karin kayan tallafi zuwa lokacin da za a cire takunkumin baki daya.

KU KARANTA KUMA: Ramadan: FG ta bukaci musulmi su cigaba da bin dokokin kare kai daga coronavirus

A wani labari na daban, mun ji cewa wani Kansila a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja ya bace bat da kayan abinci da aka bashi ya rabawa mutanen yankinsa domin saukake radadin dokar zama a gida da gwamnati ta sanya.

Gwamnatin jihar ta sanya dokar ta baci ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar. An nemi Kansilan an rasa bayan bashi buhuhunan kayan hatsi 30 da aka bukaci ya rabawa mutane.

The Nation ta tattaro cewa Kansilan na cikin kwamitin da aka nada domin rabawa mutane kayan masarufi a yankin.

Sakataren gwamnatin jihar wanda shine shugaba kwamitin yakin COVID-19 a jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da aukuwan haka kuma yace wannan abin takaici ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel