Covid-19: Ganduje ya shiga rudani kan shawarar rufe Kano

Covid-19: Ganduje ya shiga rudani kan shawarar rufe Kano

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin jahar Kano na cikin rudani a yanzu haka, kan shirin rufe jahar gaba daya domin hana yaduwar annobar COVID-19

A ranar Asabar da ya gabata ne gwamnan jahar, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da batun samun mutum na farko da ke dauke da cutar coronavirus a jahar.

Wani babban jami’in gwamnati, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa a yanzu haka gwamnan wanda ke cikin tsaka mai wuya na kan tattaunawa da gwanaye a harkar lafiya a ciki da wajen jahar, Cewar The Nation

Ya kara da cewa babban shawarar da ake bashi shine cewa a rufe jahar na tsawon makonni biyu.

Covid-19: Ganduje ya shiga rudani kan shawarar rufe Kano

Covid-19: Ganduje ya shiga rudani kan shawarar rufe Kano
Source: Twitter

Majiyar ta ce: “An fara bin tsarin gano wadanda ya yi mu’amala da su, amma hakan na da ka’idarsa saboda mai cutar ya yi mu’amala da mutane da yawa tun bayan dawowarsa jahar kafin a tabbatar da yana dauke da cutar a ranar Asabar.”

Ta ci gaba da cewar “wani abun damuwa kuma shine cewa mai cutar ya halarci wani asibiti mai zaman kansa inda likitoci suka kula dashi yayinda suke kula da sauran marasa lafiya.”

Gwamnan ya kuma bayyana cewa mutumin ya kuma halarci wata cibiyar bincike mai zaman kanta a jahar, inda aka dauki samfurinsa tare da na sauran marasa lafiya.

Gwamna Ganduje ya kuma tabbatar da cewar mutumin ya halarci bukukuwan aure da kuma sallar Juma’a a masallacin Da’awah da na Dan Adalan Kano, tun bayan dawowarsa jahar.

Kuma abu mafi hatsari a dukka lamarin shine cewa mutane na ta tururuwar zuwa gidansa ko bayan da rashin lafiyarsa tayi tsanani.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyun siyasa sun kashe miliyan N800 a iya kotun koli

A wani labarin kuma mun ji cewa gwamnonin jihohin arewa sun gudanar da wani taro domin tattauna tasirin annobar cutar covid-19 a yankin.

An gudanar da taron ne ta hanyar amfani da fasahar kiran waya na bidiyo mai hada mutane da yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel