Sojoji sun tare dumbin matafiya a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja

Sojoji sun tare dumbin matafiya a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja

Sojoji da ke kula da wata tashar bincike a Kwali a jiya Litinin,13 ga watan Afrilu, sun tare matafiya da ke shiga Abuja daga yankin Lokoja

An tattaro cewa sojoji sun tsare ababen hawa da dama, musamman motocin haya da ke cike da fasinjoji da manyan motocin daukar kaya a tashar binciken.

Wasu fasinjoji da suka gaza jure tsayuwa a karkashin zafin rana sai suka sauka daga motocin, inda suka samu babura suka hau sannan suka ci gaba da tafiyarsu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, an sa wasu masu mota da suka yi kokarin guje ma tashar binciken sojin ta hanyar yin tukin da ya saba doka a daya bangaren titin juyawa.

Motocin manyan mutane da jami'an tsaro da ke binsu a baya kawai aka bari suka wuce.

Sojoji sun tare dumbin matafiya a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja
Sojoji sun tare dumbin matafiya a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja
Asali: Twitter

Sai dai kuma, wasu ababen hawa daga yankunan Gwagwalada da Lokoja sun bi daji inda suka bi ta garin Kwali domin guje ma tashar binciken.

Wasu daga cikin direbobin da suka zanta da manema labarai, sun bayyana cewa suna sane da dokar hana shige da fice, amma cewa sun kwashi fasinjoji ne domin su samu su ciyar da iyalansu.

Wani direba, Aliyu Bala, ya ce ya kwaso fasinjoji daga Lokoja zuwa Zuba, domin ya samu kudin asibitin mahaifiyarsa da ke kwance tsawon makonni biyu.

“Bani da zabin da ya wuce shiga hatsarin da kuma kwasar fasinjoji, domin na samu kudin asibitin mahaifiyata da ke rashin lafiya a Lokoja,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

A gefe guda mu ji cewa hayaniya ta barke a wasu wurare a jihar Legas sanadiyyar matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na tsaiwaita zaman kulle.

Bisa dukkan alamu wannan mataki na kara wa’adin takunkumin zaman gidan bai yi wa mutanen Shasha, Orisunbare, Idimu, da irinsu Yankin Ejigbo da ke Jihar Legas dadi ba.

Rahoton ya ce ta’adin da aka yi a Ranar Litinin ya yi kama da abin da ya auku a Ranar Lahadi inda wasu ‘yan iskan Gari su ka buge da fashi da makami a jihohin Legas da kuma Ogun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel