‘Yan iskan Gari sun tada hayaniya a Legas dalilin kara wa’adin takunkumin kulle

‘Yan iskan Gari sun tada hayaniya a Legas dalilin kara wa’adin takunkumin kulle

A farkon makon nan ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tsawaita takunkumin da ta sa a wasu yankunan kasar domin hana yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya

Rahotanni daga jaridar The Sun sun bayyana cewa hayaniya ta barke a wasu wurare a jihar Legas sanadiyyar matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na tsaiwaita zaman kulle.

Bisa dukkan alamu wannan mataki na kara wa’adin takunkumin zaman gidan bai yi wa mutanen Shasha, Orisunbare, Idimu, da irinsu Yankin Ejigbo da ke Jihar Legas dadi ba.

Rahoton ya ce ta’adin da aka yi a Ranar Litinin ya yi kama da abin da ya auku a Ranar Lahadi inda wasu ‘yan iskan Gari su ka buge da fashi da makami a jihohin Legas da kuma Ogun.

A Ranar 12 ga Watan Afrilu, ‘yan fashi dauke da makamai sun aukawa yankunan Mangoro, Ogba, Agege, Iyana Ipaja da kuma Dopemu, su ka yi wa Bayin Allah sata a cikin duhun dare.

KU KARANTA: Mutanen Jihar Ekiti za su kara zaman kwanaki 14 a cikin gidajensu

‘Yan iskan Gari sun tada hayaniya a Legas dalilin kara wa’adin takunkumin kulle

Wasu ‘Yan iska sun rikita Legas saboda Gwamnati ta ce a zauna a gida
Source: Twitter

Wadannan fustattun ‘yan iskan Gari sun shiga lunguna da sakonnin unguwannin Legas su na aukawa Bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba, domin huce takaicin da su ke ciki.

Jaridar ta kuma bayyana cewa wadannan Mutane sun rika fasa shagunan Jama’a su na sace kayan da su ka samu. Haka zalika an yi wa wasu mutane fashi a wannan ruguntsumi.

Wani mazaunin kauyen da ake kira Aluminium a garin Dopemu ya shaidawa ‘Yan jarida cewa ‘yan fashin sun zo yankinsu ne a kan babura 30 da motoci fiye da 100 da karfe 7:00.

‘Yan fashin sun fasa shaguna da gidajen jama’a kamar yadda mazaunin kauyen ya shaida. A garin Mangoro ma dai irin wadannan ‘Yan fashi sun yi wa jama’a kwacen jakunkuna.

Irin haka ya faru a Iyana Ipaja, wanda hakan ya sa matasan yankin su ka daina barci. A yankin Agege ma akwai jita-jitar cewa ‘Yan fashi sun shiga sun yi ta’adi na kusan sa’a guda.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel