Farfesa Ayodele Adeleye ya na ikirarin ya gano maganin cutar Corovirus

Farfesa Ayodele Adeleye ya na ikirarin ya gano maganin cutar Corovirus

A Ranar Litinin 13 ga Watan Afrilun 2020, Farfesa Ayodele Adeleye ya fito ya na da’awar cewa ya na da kwayar maganin da ke warkar da cutar COVID-19 da ta addabi Duniya.

Ayodele Adeleye wanda kwararren mai bincike ne ya bayyana cewa kimiyya ta jarraba wannan magani da ya kirkiro, kuma a shirya ya ke ya fara jarraba su a kan marasa lafiyan.

Adeleye tsohon Malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma ya yi aiki a matsayin Mai bincike a babban asibitin koyarwa na Jami’ar ta Ahmadu Bello Shika, a Kaduna.

Farfesan ya shaidawa ‘Yan jarida a wani taron Manema labarai da ya kira jiya cewa ya tabbata wannan magani da ya kirkiro zai warkar da cutar COVID-19 bayan kwanaki uku.

Ya ce: “Idan gwamnati ta kawo mani mutum biyar masu COVID-19, zan warkar da su a gaban ku (‘Yan jarida). Zai dauki kwanaki uku zuwa biyar kafin mai cutar ya warke tsaf.”

KU KARANTA: CORONAVIRUS: Buhari ya bayyana matsayar Gwamnatin Tarayya

Farfesa Ayodele Adeleye ya na ikirarin ya gano maganin cutar Corovirus
Tsohon Masanin Jami’ar ABU Zaria ya ce maganinsa zai warkar da masu COVID-19
Asali: UGC

Farfesa Adeleye yace, da wannan magani da ya samo, annobar COVID-19 za ta zama tarihi.

Yanzu abin da ake bukata shi ne a samu wadanda za a jarraba maganin a kansu.

“Kusan mutane biyar har da wasu tsofaffin Dalibaina da su ka san ni da bincike su ka rika kira na, su na tambaya ko na samu wani magani da zai iya warkar da cutar COVID-19.”

“Wani daga cikin wanda cutar ta kama ya kasance ya na fama da wahalar numfashi, bayan mintuna 10 da shan wannan magani, ya fara samun sauki.

“Mun fada masa ya cigaba da zuwa na kwanaki biyar. Sai mu ka ce masa ya je gwaji, kuma ya samu sauki. Da da shi za mu yi hirar nan, amma shi mutum mai kunyar jama’a ne.” Inji Farfesa Adeleye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng