An sake sallamar mutane 6 da suka warke daga cutar covid-19 a Najeriya
Gwamnatin jihar Legas ta sanar da sallamar karin wasu mutane 6 da suka samu warkewa daga cutar covid-19, kamar yadda gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, ya sanar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
"A yau (Litinin), an sake sallamar wasu mutane 6 bayan an tabbatar da samun saukinsu. Mutanen Shidda; mace daya da maza biyar, an sallamesu ne daga cibiyar killacewa da ke cikin asibitin cututtuka masu yaduwa (IDH) da ke unguwar Yaba a garin Legas.
"Wanna lamari ya faranta mana rai tare da bamu karin karfin gwuiwa, saboda yanzu adadin mutanen da suka warke daga cibiyoyinmu daban-daban ya kai 61.
"Hakan ya nuna cewa idan mu ka hada karfi wuri guda, za mu samu galaba a kan cutar covid-19. Ba za mu gaza ba har sai mun cimma nasara.
"Ina yi muku godiya bisa cigaba da juriya da ku ke yi a wannan lokaci na matsi. Na tabbata wannan sadaukarwar da mu ke yi, ba za ta fadi kasa a banza ba," a cewarsa.
Warkeware mutanen na zuwa a daidai lokacin da Melinda Gates, uwargidar biloniya Bill Gates ta yi gargadin cewa idan har duniya bata dauki matakin gaggawa da ya dace ba, toh shakka babu za a tsinci gawarwaki a fadin unguwanni a Afrika.
Melinda ta yi wannan kira ne yayinda ta ke jawabi ga CNN a kan annobar coronavirus da tasirinta a kasashen duniya.
DUBA WANNAN: Kauran Bauchi ya bayyana halin da ya shiga a cibiyar killacewa bayan ya kamu da covid-19
Ta ce zuciyarta na a Afrika, inda ta bayyana cewa ta damu matuka domin ba lallai ne nahiyar ta iya magance barnar cutar ba.
“Annobar za ta munana a kasashe masu tasowa.
“Dalilin da yasa har yanzu kuke ganin kamar mutanen da suka kamu a nahiyar basu da yawa, ya kasance saboda basu da wuraren gwaji da yawa.
“Duba abunda ke faruwa a kasar Ecuador, suna ajiye gawarwaki a unguwanni, za ku ga faruwar hakan a kasashen Afrika,” in ji uwargida Melinda.
Melinda Gates, wacce ta kasance jigo a gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, ta nuna tsoron cewa abubuwa na iya tabarbarewa a Afrika da zaran lamarin ya girmama, saboda tabarbarewar tsarin lafiyarsu da rashin agaji.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng