COVID-19: Gawarwaki zasu mamaye titunan kasashen Afirka idan aka yi wasa - Gate

COVID-19: Gawarwaki zasu mamaye titunan kasashen Afirka idan aka yi wasa - Gate

- Melinda Gates ta yi hasashen samun gawarwakin mutane birjik a titunan kasashen Afirka sakamakon COVID-19

- Ta ce hakan zai kasance ne idan har duniya bata yi gaggawan daukar mataki kan cutar ta corronavirus ba

- A cewarta ba lallai bane nahiyar ta iya tunkarar lamarin idan har ya yi mata daurin talala

Melinda Gates, Uwargidar biloniya Bill Gates ta yi gargadin cewa idan har duniya bata dauki matakin gaggawa da ya dace ba, toh shakka babu za a tsinci gawarwaki a fadin unguwanni a Afrika.

Misis Gates ta yi wannan kira ne yayinda ta ke jawabi ga CNN, kan coronavirus da tasirinta a kasashen duniya.

COVID-19: Gawarwaki zasu mamaye titunan kasashen Afirka idan aka yi wasa - Gate
COVID-19: Gawarwaki zasu mamaye titunan kasashen Afirka idan aka yi wasa - Gate
Asali: Twitter

Ta ce zuciyarta na a Afrika, inda ta bayyana cewa ta damu matuka domin ba lallai ne nahiyar ta iya magance barnar cutar ba.

“Zai munana a kasashe masu tasowa.

“Dalilin da yasa har yanzu kuke ganin kamar mutanen da suka kamu a nahiyar basu da yawa, ya kasance saboda basu da wuraren gwaji da yawa.

“Duba abunda ke faruwa a Ecuador, suna ajiye gawarwaki a unguwanni, za ku ga faruwar hakan a kasashen Afrika,” in ji Misis Gates.

Melinda Gates wacce ta kasance jigo a gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation ta nuna tsoron cewa abubuwa na iya tabarbarewa a Afrika da zaran lamarin ya girmama, saboda tabarbarewar tsarin lafiyarsu da rashin agaji.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga al’umman Najeriya a yau Litinin

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata uwa mai yara biyar da aka ambata da suna, Shabnum Sadiq ta mutu bayan ta kamu da coronavirus a lokacin wani tafiya da ta yi zuwa kasar Pakistan.

Matar mai shekara 39 a duniya ta rasu a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da rashin lafiya sakamakon mummunan cutar, Metro ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa matar wacce ta yi aiki a majalisar Slough Borough, Ingila, ta mutu ta bar mijinta da yara biyar, ciki harda 'yan hudu masu shekaru 13.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel