Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar

Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar

- Cutar coronavirus ta halaka wata uwa mai yara biyar da aka ambata da suna Shabnum Sadiq

- An tattaro cewa matar mai shekaru 39 ta kwashi cutar ne a yayin wani tafiya da ta yi zuwa Pakistan

- Marigayiyar, wacce ta kasance mai ba da shawara a Slough, Ingila, ta bar yara biyar ciki harda 'yan hudu

Wata uwa mai yara biyar da aka ambata da suna, Shabnum Sadiq ta mutu bayan ta kamu da coronavirus a lokacin wani tafiya da ta yi zuwa kasar Pakistan.

Matar mai shekara 39 a duniya ta rasu a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da rashin lafiya sakamakon mummunan cutar, Metro ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa matar wacce ta yi aiki a majalisar Slough Borough, Ingila, ta mutu ta bar mijinta da yara biyar, ciki harda 'yan hudu masu shekaru 13.

Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar

Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar
Source: UGC

Jigon majalisa James Swindlehurst ya ce: “Hakan ya taba zuciyarmu gaba daya sannan tunaninmu na tare da iyalai da abokanta.

“Shabnum ta kasance mai bada shawara da ta jajirce kan aiki, kuma duk da cewar wannan ne zangonta na farko, ta bayar da gudunmawa fiye da shekarun da ta yi a zauren majalisar.

“Mun yi aiki tare kai da fata kuma, nayi kewanta sosai. Wannan gagarumin rashi ne ga majalisar da garin, amma hakan bai kai rashin da iyalanta da makusanta suka yi ba."

KU KARANTA KUMA: Dokar hana fita: Hankula sun tashi a Legas yayinda yan fashi ke kai farmaki gida-gida

A wani rahoton kuma, mun ji cewa gwamnatin jahar Lagas a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, ta tabbatar da mutuwar wani mara lafiya sakamakon cutar coronavirus a jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi, wanda ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya ce a yanzu mutane biyar kenan suka mutu a jahar.

Ya ce mutumin ya rasu ne sakamakon tabarbarewar lafiya da ke da nasaba da coronavirus.

Abayomi ya kara da cewa an samu sabbin mutane 11 da suka kamu a ranar Asabar. A yanzu jahar na da jimlar mutane 177 da suka kamu da COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel