Covid-19: 'Yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnati da suka karya dokar hana taro

Covid-19: 'Yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnati da suka karya dokar hana taro

'Yan sanda a jihar Nasarawa sun kama manyan jami'an gwamnatin jihar da suka karya dokar da gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya kafa a kan killace kai tare da hana taron jama'a saboda dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Manyan jami'an gwamnatin da aka kama sune; Alhaji Suleman Agyo, shugaban karamar hukumar Lafiya ta kudu da Mukhtar Wakeel, mukaddashin rijistara a kwalejin kimiyya da fasaha da ke garin Lafiya.

Faifan bidiyon bikin auren shugaban karamar hukumar ya yadu a dandalin sada zumunta, musamman a tsakanin mazauna garin Lafiya.

Da ya ke tabbatar da kama manyan jami'an gwamnatin a ranar Lahadi, kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, Bola Longe, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin sabawa umarnin gwamnatin jiha.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun kwana a hannun jami'an 'yan sanda na ofishin 'Division "A", a jihar.

Covid-19: 'Yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnati da suka karya dokar hana taro
Abdullahi Sule; gwamnan jihar Nasarawa
Asali: UGC

Kazalika, rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa tana neman wasu manyan jami'an gwamnatin jihar da suka halarci taron bikin, amma kuma suka tsere bayan jin labarin an kama abokansu.

Manyan jami'an gwamnatin da ake nema sune; Alhaji Suleiman Wambai, shugaban mataimakin jam'iyyar APC na kasa shiyyar arewa ta tsakiya da shugaban karamar hukumar Lafia ta gabas, Shuaibu Buba.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 9, sun kubutar da mutane 18 a Zamfara

Rundunar 'yan sanda ta ce halayyar manyan jami'an gwamnatin, na halartar taron jama'a da yawansu ya zarce 20, ta sabawa matakin da gwamnati ta dauka domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19 a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar ya ce dole doka ta yi aiki a kan manyan jami'an gwamnatinsa, a saboda haka ba zai saka baki domin a sakesu ba.

Kazalika, a ranar Lahadi, kwamishinan shari'a na jihar, Jastis Dakta Abdulkarim Kana, ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust batun kama manyan jami'an gwamnatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel