Dokar hana walwala: Jama'a sun yanke hannun dan sanda, sun raunata wasu

Dokar hana walwala: Jama'a sun yanke hannun dan sanda, sun raunata wasu

Rahotanni daga kasar Indiya sun bayyana cewa an yankewa wani dan sanda hannu tare da raunata wasu abokan aikinsa yayin da su ke kokarin tabbatar da dokar hana zirga - zirga da walwala a Punjab.

Punjab jiha ce da ke arewacin kasar Indiya.

Direbobi ne suka fito daga motocinsu tare da kai wa 'yan sandan hari a daidai wani shingen kan hanya domin binciken ababen hawa. Lamarin ya faru ne a unguwar Patila a lokacin da 'yan sandan suka tsayar da motoci a shingen.

BBC ta rawaito cewa an kama uku daga cikin wadanda su ka kai harin, wadanda aka bayyana cewa 'yan wata kungiya ce ta addini.

"Maharan su na dauke da wukake da takobi, amma daga bisani sun mika wuya bayan an fafata na tsawon sa'a biyu," a cewar shugaban 'yan sandan Punjab yayin hirarsa da gidan talabijin na NDTV.

Dokar hana walwala: Jama'a sun yanke hannun dan sanda, sun raunata wasu
Dakin gwajin cutar covid-19
Asali: UGC

Wannan ba shine karo na farko da jama'a a sassan Indiya su ka kai hari a kan jami'an 'yan sanda ba yayin da su ke kokarin tirsasasu yin biyayya ga dokar zama a gida da aka saka domin dakile yaduwar annobar cutar coronavirus.

A nan gida Najeriya ma, wasu gungun 'yan fashi da makami su 6 sun kai hari a kan shingen kan hanya na jami'an 'yan sanda a Enugu, tare da yin awon gaba da bindigu kirar Ak47.

DUBA WANNAN: An tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin wani mai gadi da ya yi mu'amala da mutane ba iyaka a Kaduna

Tawagar 'yan fashin sun kai harin ne a cikin babur mai kafa uku da aka fi sani da 'keke', inda suka raunata 'yan sanda uku tare da kone musu motar sintiri.

Jaridar Punch ta rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar Talata a kan hanyar Enugu zuwa Nsukka a yayin da 'yan sandan suka tsare hanyoyi domin tilasta wa jama'a biyayya ga dokar hana zirga-zirga da walwala saboda annobar covid-19.

Wata majiya a cikin jami'an tsaro ta sanar da Punch cewa 'yan ta'addar, sanye cikin bakaken kaya, sun fara kai harin ne a kan shingen kan hanya da ke Ekwegbe, inda suka raunata wani dan sanda mai suna Insifekta James.

'Yan ta'addar sun kara kai wa wasu 'yan sandan hari a shingen kan hanya na gaba da suka tarar a kan hanyar Enugu zuwa Nasukka, inda suka raunata 'yan sanda guda biyu tare da yin awon gaba da bindigunsu kirar Ak47.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng