Kano: An takaita Keke-Napep, watakila Gwamnati ta rufe Masallatai da Coci

Kano: An takaita Keke-Napep, watakila Gwamnati ta rufe Masallatai da Coci

A cikin karshen makon nan ne aka tabbatar da cewa an samu wani mai dauke da kwayar cutar Coronavirus a jihar Kano. Wannan ne karon farko da cutar ta bayyana a Kano.

Wani Dattijo wanda ya taba rike Jakadan Najeriya a kasar waje ne aka samu ya na dauke da wannan cuta. Ana zargin cewa wannan Bawan Allah ya kamu da cutar ne a Legas.

A dalilin haka ne gwamnatin jihar Kano ta yi wuf ta fara daukar matakai domin kare rayukar dinbin miliyoyin mutanen da ke zaune a garin Kano daga wannan muguwar cuta.

Wannan labari ya zo ne a daidai lokacin da hukumar NCDC mai takaita yaduwar cuta ta kafa dakin gwajin COVID-19 a asibitin koyon aiki na Malam Aminu Kano da ke Jihar.

Kwamishinan kiwon lafiya na Kano, Dr. Ibrahim Tsanyawa, ya fadawa Daily Trust cewa an hana masu Keke-Napep watau 'a-daidaita-sahu' daukar fiye da fasinja guda a lokaci daya.

KU KARANTA: Jihohi 17 da har yanzu ba a samu wanda ya kamu da COVID-19 ba

Kano: An takaita Keke-Napep, watakila Gwamnati ta rufe Masallatai da Coci

Za a dauki mataki bayan samun bullar cutar coronavirus a jihar Kano
Source: Twitter

A yunkurin hana yaduwar cutar, Dr. Ibrahim Tsanyawa ya shaidawa Jaridar cewa hukuma za ta hukunta duk Direban Keke-Napep din da aka samu dauke da mutum fiye da guda.

Haka zalika gwamnatin Kano ta ce akwai yiwuwar a rufe duk wasu Masallatai da Coci da ke jihar idan har dalili ya sa hakan. Kawo yanzu dai ba a dauki wannan mataki ba tukuna.

“Kwamitin yaki da annobar cutar COVID-19 zai gana da manyan Limaman Masallatan Juma’a da manyan Fastocin da ke Limanci a coci domin jin yadda za a rika ibada a dakuna.”

Kwamishinan ya bayyana cewa wannan zama da za ayi da Malaman addini zai sa gwamnati ta dauki matakin hanyar da za a bi na hana yaduwar wannan kwayar cuta a jihar Kano.

“Idan taron ya kai mu ga rufe Masallatai da Cocin da ke jihar, za mu yi haka, domin kare rayukan mutanenmu.” A halin yanzu dai ana cigaba da tsaurara matakan fita a fadin Jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel