'Na ji jiki', Kauran Bauchi ya bayyana halin da ya shiga a cibiyar killacewa bayan ya kamu da covid-19

'Na ji jiki', Kauran Bauchi ya bayyana halin da ya shiga a cibiyar killacewa bayan ya kamu da covid-19

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa ya sha matukar wuya a cikin sati uku da ya shafe a cibiyar killacewa baya an tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.

Da ya ke magana da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Bauchi ranar Asabar, gwamnan ya ce halin da ya tsinci kansa a ciki ya sauya rayuwarsa har abada.

Gwamnan ya mika godiya ga wadanda suka nuna damuwarsu a kan halin da ya shiga tare da mika wata godiyar ga masoyansa da su ka cigaba da bashi goyon baya a yayin da ya ke a killace.

"Wannan cuta da ta kamani ta bar min tabo a rayuwata. Na sha wahala, na ji jiki a cibiiyar killacewa, ji nake tamkar ba ni da kowa, amma so da kauna da mutanen Bauchi suka nuna min ya bani matukar karfin gwuiwa," a cewarsa.

Sannan ya cigaba da cewa, "ina mai godiya ga Allah da ya rabani da wannan muguwar cuta. Ina mai bawa jama'ar Bauchi da na Najeriya hakuri a kan abinda ya faru, ni ma bada son raina cutar ta kamani ba.

'Na ji jiki', Kauran Bauchi ya bayyana halin da ya shiga a cibiyar killacewa bayan ya kamu da covid-19
Bala Mohammed a masallacin Juma'a
Asali: Twitter

"Na samu sakonnin jaje, fatan alheri da addu'o'i daga mutane daban-daban, wasu ma ban sansu ba.

"Irin kauna da soyayyar da na gani daga wurin mutane, sun kara min kaimi wajen yi wa jama'ar Bauchi aiki tukuru, kuma ina mai tabbatarwa da jama'a cewa zan yi hakan, kamar yadda na ci al washi."

DUBA WANNAN: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

Kazalika, gwamnan ya bukaci masoya da magoya bayansa a kan kar su damu da zuwa duba shi a gidan gwamnati, tare da bayyana cewa tuni ya samu sakonni da fatan alherin da suke yi masa.

A ranar Alhamis ne aka sallami Bala Kaura daga cibiyar killacewa bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa yanzu ba ya dauke da kwayar cutar covid-19.

Sai dai, gwamnan ya yi watsi da shawarar bukatar ya nesanta da jama'a da aka ba shi, saboda ya halarci sallar Juma'a tare da gaisawa da jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel