Alkaluman NDCS sun nuna Mutane 10 sun mutu a sanadiyyar COVID-19
A daidai lokacin da ake jimamin mutuwar sama da mutum 108, 000 a fadin Duniya, a Najeriya yanzu ne aka samu mutum na goma da cutar nan ta Coronavirus ta kashe.
Alkaluma sun tabbatar da cewa COVID-19 ta hallaka mutane 10 a kasar nan. An bayyana wannan ne a yayin da aka ji cewa an sake samun mutane 13 da su ka kamu da cutar.
Wani abin farin ciki shi akalla kashi 22% na wadanda su ka kamu da wannan muguwar cuta sun warke a Najeriya. A halin yanzu an sallami mutane 70 daga asibitocin kasar.
Wadanda su ka mutu a sanadiyyar wannan cuta kashi 3% ne kacal na wadanda su ka kamu. Daga cikin wadanda COVID-19 ta kashe kwanan nan akwai mutum daga jihar Legas.
A Ranar Asabar, 11 ga Watan Afrilu Kwamishinan lafiyan Legas ya sanar da cewa wani Bawan Allah da ke jinyar COVID-19 a asibitin koyon aiki na jami’ar jihar Legas ya rasu.
KU KARANTA: An samu Dattijon da ke dauke da COVID-19 a Jihar Kano
A daidai lokacin nan ne kuma aka ji cewa COVID-19 ta kai wata Mata mai shekaru 37 kasa a wani asibitin kudi da ke jihar Legas. Kusan mutane biyar kenan cutar ta kashe a jihar.
A cikin Watan Maris ne aka fara samun wanda ya mutu a sanadiyyar wannan cuta. Hukumar NCDC mai kokarin takaita yaduwar cuta a Najeriya ta sanar da wannan mutuwa.
Sulaiman Achimugu wanda tsohon shugaban hukumar PPMC ne ya fara yin shadada a lokacin wannan annoba. Dama can Marigayin ya na fama da ciwon sukari da cutar daji.
Wannan cuta ta ratsa jihohi akalla 19 da babban birnin tarayya Abuja. A cikin karshen makon nan ne aka samu wanda ya fara kamuwa da cutar a jihar Kano a karon farko a tarihi.
Najeriya ce ta ke dauke da kashi 0.00909090909% na mutuwar COVID-19 a Duniya. Bayan watanni wannan annoba ba ta yi kamari a Kasashen Afrika kamar yadda aka yi tunani ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng