Covid-19: Mutane uku sun kara mutuwa a Najeriya, annobar ta shiga jihohi 19
Cibiyar shawo kan cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun karin wasu mutane 13 da ke dauke da kwayar cutar covid-19 a jihohi uku.
A cikin wani jawabi da NCDC ta fitar a yammacin ranar Asabar, ta bayyana cewa an samu karin mutum daya da aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar a Legas, yayin da aka samu mutum dai - dai a jihohin Delta da Kano.
Kazalika, NCDC ta sanar da cewa karin wasu mutane uku da suka kamu da kwayar cutar sun mutu.
Ya zuwa yanzu akwai jimillar mutum 318 da ke dauke da kwatar cutar covid-19 a Najeriya, an sallami mutum 70 daga cikin adadin, yayin da mutum 10 aka sanar da cewa sun mutu.
Yanzu haka, a karo na farko, annobar cutar covid-19 ta bulla jihohin Anambara, Delta, Neja da Kano, lamarin da kawo jimillar jihohin da aka tabbatar da samun masu dauke da cutar zuwa guda 20.

Asali: UGC
Har ya zuwa tsakar ranar Juma'ar da ta gabata, jihohi 17 ne aka sanar da cewa an samu bullar annobar cutar covid-19, amma a yammacin ranar, NCDC ta sanar da bullar cutar a jihohin Neja da Anambara, kafin daga bisani a sanar da bullar annobar a jihar Kano ranar Asabar.
DUBA WANNAN: An tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin wani mai gadi da ya yi mu'amala da mutane ba iyaka a Kaduna
Anambara ce jiha ta farko da aka sanar da samun bullar annobar a yankin kudu maso gabas mai adadin jihohi 5.
Jihar Neja ta bi sahun jihar Kwara a samun mai dauke da kwayar cutar covid-19 a jihohin yankin arewa ta tsakiya mai adadin jihohi 6.
A yankin arewa maso yamma, jihar Kano ta bi sahun jihohin Kaduna da Katsina a bullar annobar cutar covid-19.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng