Ba shiga, ba fita: Gwamnan Neja ya rufe jahar bayan an samu bullar coronavirus

Ba shiga, ba fita: Gwamnan Neja ya rufe jahar bayan an samu bullar coronavirus

- Gwamnatin jahar Neja karkashin Abubakar Sani Bello, ta sanar da rufe gaba daya harkoki a jahar daga ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu

- Hakan na zuwa ne bayan an gano mutum na farko da ke dauke da cutar COVID-19 wacce aka fi sani da coronavirus a jahar

- Gwamnan ya kuma yi umurnin ci gaba da dakatar da dukkanin harkoki na addini har sai baba ya gani

Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanar da rufe gaba daya harkoki a jahar daga ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu.

Hakan na zuwa ne bayan an gano mutum na farko da ke dauke da cutar COVID-19 wacce aka fi sani da coronavirus a jahar.

Ba shiga, ba fita: Gwamnan Neja ya rufe jahar bayan an samu bullar coronavirus
Ba shiga, ba fita: Gwamnan Neja ya rufe jahar bayan an samu bullar coronavirus
Asali: UGC

A cewar kwamishinan lafiya na jahar, Dr. Muhammad Maikusidi, lamarin ya fito ne daga yankin Limawa a Minna, babbar birnin jahar.

Gwamnan ya umurci tawagar COVID-19 na jahar da su killace yankin na tsawon kwanaki 14.

Gwamnan ya kuma yi umurnin ci gaba da dakatar da dukkanin harkoki na addini har sai baba ya gani.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake samun wani da ya mutu sakamakon coronavirus a Lagas

A wani labarin kuma, mun ji cewa an samu bullar cutar Coronavirus ta farko a jihar Kano yau Asabar, 11 ga watan Afrilu 2020, kwamishanan lafiyan jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya tabbatar da hakan.

Yanzu haka ana cikin ganawa tsakanin gwamnan da mukarrabansa. Nan ba da dadewa ba gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, zai yi jawabi ga al'ummar jihar.

A cewar majiya mai siqa, mutumin da ke dauke da cutar wani tsohon jami'in diflomasiyya ne da aka kwantar a wani asibitin kudi a Kano.

An bayyana cewa mutumin ya yi daga Legas zuwa Abuja sannan ya dira a Kano.

An gwadashi ne a cibiyar gwajin dake asibitin koyarwan Aminu Kano AKTH. Tuni an garzaya da shi dakin killace mutane a Kwanar Dawaki.

A wani labarin kuma mun ji cewa n sallami mutane hudu da suka kamu da coronavirus a babban birnin tarayya Abuja bayan an musu magani sun kuma warke.

Hukumar babban birnin tarayya Abuja, FCTA, ce ta sanar da hakan cikin wani sako da ta wallafa a Twitter a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel