An tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin wani mai gadi da ya yi mu'amala da mutane ba iyaka a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da samun mutum na shidda da ke dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar.
A wani sako da kwamishinar lafiya a jihar Kaduna, Amina Mohammed Baloni, ta fitar a shafinta na Tuwita, ta ce an tabbatar da samun kwayar cutar a jikin wani mutum da ke aikin gadi a unguwar Mando.
A cewar kwamishiniyar, mutumin bai dade da dawowa Kaduna ba daga jihar Legas. Ya dawo jihar Kaduna ne a motar haya, lamarin da ke nuna cewa ya yi mu'amala da sauran fasinjojin motar da ya shiga.
A cikin sakon, Amina ta bayyana cewa an kebe mai gadin a cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta jiha bayan an tuntubi hukuma a kan tabarbarewar halin rashin lafiya da mai gadin ke ciki.
"Bai yi mu'amala da sauran mutane biyar da aka tabbatar da suna dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Kaduna ba. Mun shiga cikin damuwa da dimuwa a kan wannan batu, saboda mun tabbatar da cewa ya yi mu'ama tare da yada cutar ga mutane ma su yawa," a cewar sakon kwamishiniyar.
Sannan ta cigaba da cewa, "zai yi mutukar wuya a iya gano dukkan sauran mutanen da ya yi mu'amala da su a motar hayar da ya hau da kuma sauran mutanen da ya yi mu'amala da su tun bayan dawowarsa.
"Kwamitin ko ta kwana da aka kafa yana kokarin samun jerin sunayen mutanen da zai iya tuna ya yi mu'amala da su domin nemosu tare da bincikar lafyarsu."
Kazalika, ta bayyana cewa yanzu haka kwamitin ya fi mayar da hankalinsa wajen nemo mutane da ababen hawan da mai gadin ya yi amfani da su da ma mutanen da ya yi mu'amala da su a asibitin da ya ziyarta.
DUBA WANNAN: Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)
Kwamishinar ta kara da cewa daga yanzu gwamnatin jihar Kaduna ta hana daukan fasinja fiye da biyu a layin kujera daya a motocin haya masu daukan mutane da da yawa.
Daga yanzu, gwamnatin jihar Kaduna ta haramta wa masu kananan motoci da babura masu kafa uku daukan fasinjoji kwata-kwata, saboda basu cika ka'idojin nesanta da ake bukata domin dakile yaduwar kwayar cutar covid-19 ba, a cewar kwamishinar.
Amina ta jaddada bukatar yi wa dokar hana walwala da taron jama'a biyayya, sannan ta shawarci jama'a su bawa tsaftar jiki da muhalli muhimmanci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng