Yanzu Yanzu: An sake samun wani da ya mutu sakamakon coronavirus a Lagas

Yanzu Yanzu: An sake samun wani da ya mutu sakamakon coronavirus a Lagas

- Cutar coronavirus ta sake kashe wani mara lafiya a jahar Lagas

- Kwamishinan lafiya na jahar Lagas, Akin Abayomi ne ya sanar da labarin mutuwar a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu

- Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da bin dokar nisantar taron jama'a domin tsira

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa cutar coronavirus ta sake kashe wani mara lafiya a jahar Lagas.

Kwamishinan lafiya na jahar Lagas, Akin Abayomi ne ya sanar da labarin mutuwar a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu.

A cewar kwamishinan, mara lafiyan ya mutu ne a wani asibiti mai zaman kansa.

“Mun cika da bakin ciki a kan mutuwar wani mara lafiya sakamakon cuta da ke da nasaba da COVID-19 a wani asibiti mai zaman kansa a Lagas. Dan Allah ku ci gaba da bin dokar nisantar taron jama’a domin tsira,” in ji shi.

A yanzu jimlar mutane hudu kenan suka mutu a jahar Lagas, yayinda suka zaman takwas a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO

A wani rahoton kuma, mun ji cewa 'yan Najeriya, mazauna Abuja, da ya kamata su ci moriyar tsarin bayar da tallafi don rage radadi da matsin tattalin arziki da annobar cutar covid-19 ta haifar, sun musanta cewa an ba su tallafin kudi ko kuma na kaya daga wurin gwamnati.

Ministar walwala da jin dadin jama'a, Sadiya Umar Farouq, ta ce talakawan Najeriya da masu karamin karfi miliyan 2.6 sun ci moriyar shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya.

Ta bayyana cewar kimanin gidaje miliyan 11 aka zaba tare da ba su tallafin kudi a jihohin Najeriya 35.

Ministar ta ce an zabi gidajen talakawa 5,982 da aka bawa talllafin a Abuja, gidajen talakawa 8,271 a jihar Nasarawa, 6,732 a jihar Katsina, da kuma jihar Anambra inda gidajen talakawa 1,367 suka ci moriyar shirin.

Amma duk da hakan, wani bincike da jaridar SaharaReporters ta yi ikirarin cewa ta gudanar a tsakanin talakawa da masu karamin karfi mazauna yankin Dutsen Alhaji, Kuje, Gwagwalada da Gudu a Abuja, ya gano cewa jama'a ba su da masaniyar an raba N20,000 a matsayin tallafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel