Ngozi Okonjo Nwela; Tsohuwar ministar PDP ta samu babban mukami a IMF

Ngozi Okonjo Nwela; Tsohuwar ministar PDP ta samu babban mukami a IMF

Hukumar lamunin kudi ta kasa da kasa (IMF) ta nada Ngozi Okonjo-Iweala, tsohuwar ministar kudi a gwamnatin PDP lokacin mulkin Obasanjo da Jonathan, a matsayin mai bayar da shawara a harkokin waje.

Tsohuwar ministar za ta yi aiki ne a matsayin mamba a karkashin kungiyar da ke bawa Kristalina Georgieva, manajan darektan IMF, shawarwari.

A kwanakin baya bayan nan ne kasar Afrika ta Kudu ta nada Okonjo-Iweala a matsayin mamba a kwamitin da zai ke bawa shugaban kasarsu shawara a kan harkokin tattalin arziki.

A cikin sanarwar nadin, Georgieva ta ce mambobin kungiyar za su ke haduwa lokaci zuwa lokaci domin bayar da shawarwarin da za su kawo cigaba da samar da sabbin tsare-tsare a IMF.

Ngozi Okonjo Nwela; Tsohuwar ministar PDP ta samu babban mukami a IMF

Ngozi Okonjo-Nweala
Source: Depositphotos

"Tun kafin yaduwar annobar covid-19 da ta shafi harkokin kudi da tattalin arziki, mambobin IMF su na fuskantar manyan kalubale ma su wuyar sha'ani.

DUBA WANNAN: NSIP: Hadimar Buhari ta mayarwa da Lawan da Gbajabiamila martani a kan sukar shirin bayar da tallafi

"Domin samun damar sauke nauyin da ke rataye a wuyanmu a IMF, mu na bukatar hannun kwararru daga bangarori da dama.

"A saboda haka, ina mai alfahari da farincikin sanar da wata kungiyar kwararru, a harkokin kasuwa da kudi, a matsayin masu bayar da shawara daga waje a harkokin IMF. Mun tabbata cewa za mu karu daga dumbin ilimi da gogewar da suke da ita," a cewarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel