Ba shiga, ba fita: An rufe Daura bayan an tabbatar da samun mutane 3 da cutar covid-19

Ba shiga, ba fita: An rufe Daura bayan an tabbatar da samun mutane 3 da cutar covid-19

Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin rufe karamar hukumar Daura; ba shiga, ba fita, bayan an tabbatar da samun mutane uku da suke dauke da kwayar cutar covid-19.

Sanarwar rufe jihar ta fito ne a yau, Juma'a, kamar yadda jaridu da dama a fadin kasa suka wallafa.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ne ya bayar da umarnin rufe karamar hukumar bayan an tabbatar da bullar annobar covid-19 a yankin.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

A jerin wasu sakonni da aka wallafa a shafin Tuwita, Masari ya ce an tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin mata da 'ya'yan likitan da kwayar cutar covid-19 ta kashe a Katsina a cikin satin nan.

Masari ya bayyana cewa an tura jinin mutane 23 domin gudanar da gwaji a kansu bayan mutuwar likitan, kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa matarsa da 'ya'yansa sun kamu da kwayar cutar.

Ba shiga, ba fita: An rufe Daura bayan an tabbatar da samun mutane 3 da cutar covid-19

Buhari da Masari
Source: UGC

Gwamnan ya ce, gwamnati za ta bayar da tallafi ga mazauna karamar hukumar na tsawon lokacin da dokar za ta cigaba da aiki.

DUBA WANNAN: Za a killace duk wanda aka kama ya shiga jihar Kaduna - Gwamna

"Za mu cigaba da sa ido da bibiyar al'amura. Ba za mu yi kasa a gwuiwa ba wajen saka dokar rufe duk wata karamar hukuma da aka tabbatar da samun bullar annobar covid-19 ba. Ita kanta jihar za mu iya rufeta gaba daya idan yanayi ya nuna akwai bukatar yin hakan.

"Za mu bar shagunan sayen magani da na kayan abinci guda uku, wadanda jama'a za su ke sayen kaya a wurinsu bisa sa idon hukuma domin tabbatar da biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar cutar," a cewar Masari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel