Gwamna Zulum ya yi ganawar sirri da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa

Gwamna Zulum ya yi ganawar sirri da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa

- Gwamna Babagana Zulum ya kai ziyara fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya Abuja

- Zulum ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yaki da Boko Haram a jaharsa

- Gwamnan ya taso ne daga Maiduguri, babbar birnin jahar Borno a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu.

A ziyarar da ya kai, Zulum ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bayani daga tawagar labaran gwamnan, ya nuna cewa, tattaunawar shugabannin ya karkata ne ga yadda jahar Borno ke yaki da Boko Haram.

Sun kuma zanta kan kokarin da yake yi na ganin ya gina zaman lafiya, mayar da yan gudun hijira muhallinsu da kuma farfado da tattalin arzikin jahar.

Gwamnan dai ya baro Maiduguri a ranar Alhamis, ta jirgi na musamman da ya yi daidai da umurnin fadar shugaban kasa kan rufe harkoki da aka yi a Abuja saboda COVID-19.

Hakan ya sa aka hana zirga-zirga amma bai shafi muhimman abubuwa ba.

A yayin ganawar nasu, Zulum ya sanar da shugaban kasar bayanai a kan halin da jaharsa ke ciki.

Ga hotunan ganawar nasu a kasa:

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya warke daga Coronavirus

A wani labarin kuma, mun ji cewa kasar Najeriya da jamhuriyar Chadi a ranar Alhamis sun amince da jaddada yarjejeniyar yakar Boko Haram da ke tsakaninsu.

Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi mai murabus ya sanar da hakan ne a taron da aka yi tsakanin hukumomin kasashen biyu a Abuja.

Ya ce yana farin cikin jaddada yarjejeniyar da ke tsakaninsu don ci gaba da tabbatar da nasarar jami'an tsaron hadin guiwa.

Ya ce kirkirar MNJTF da kasashen suka yi ya kawo babbar nasara wajen yaki da ta'addanci. Ya ce akwai bukatar su jaddada yarjejeniyar.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, mayakan Boko Haram din sun addabi yankin Arewa maso gabas din ne tun 2009.

Daga bisani ne suka tsallaka kasashen Nijar, Chadi da Kamaru, wanda ya jawo gaggawar daukar mataki.

Ministan ya ce duk da nasarorin da aka samu wajen yakar ta'addancin, Najeriya tayi matukar damuwa da yadda 'yan ta'addan ke ci gaba da kaiwa dakarunta hari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel