Congo: 'Yan sanda sun kama shugaban ma'aikatan shugaban kasa

Congo: 'Yan sanda sun kama shugaban ma'aikatan shugaban kasa

Rahotanni sun kawo cewa jami’an ‘yan sanda sun kama shugaban ma'aikatan shugaban kasar Dimokradiyyar Congo a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu, a Kinshasa, babban birnin kasar awowi da dama bayan an yi masa tambayoyi kan zargin kashe kudi ba bisa ka'ida ba.

Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa an yi wa Vital Kamerhe tambayoyi kan rawar ganin da ya taka a kan zargin cin hanci a kwangilar gudanar da manyan ayyuka, wanda ke a karkashin kulawarsa a kwanaki 100 na wa'adin da ya wuce na jagorancin Shugaba Félix Tshisekedi's a bara.

An tattaro cewa an tisa keyarsa zuwa babban gidan yarin kasar na Makala, inda ya kwana a chan.

Sai dai ba a sani ba ko za a tuhume shi a kan zarge-zargen.

Congo: 'Yan sanda sun kama shugaban ma'aikatan shugaban kasa
Congo: 'Yan sanda sun kama shugaban ma'aikatan shugaban kasa
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato mai magana da yawun Shugaba Tshisekedi yana cewa "shugaban kasa ba ya tsoma baki a kan harkokin da suka shafi shari'a".

Magoya bayan Mista Kamerhe sun yi zanga-zanga a mahaifarsa da ke Bukavu, a gabashin kasar Dimokradiyyar Congo sannan suka toshe hanyar shiga hedikwatar jam'iyyarsa.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta karbi sawu na 2 na kayan agajin annobar Coronavirus daga China

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kasar Afirka ta kudu, Mista Cyril Ramaphosa ya dakatar da ministar sadarwa, Stella Ndabeni Abrahams, na tsawon watanni 2 sakamakon kamata da aka yi da laifin karya dokar hana shige da fice da zirga zirga a yayin marran annobar Coronavirus.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito fadar shugabank kasar Afirka ta kudu ta bayyana daga cikin watanni biyu da shugaba Ramaphosa ta dakatar da Stella, ba za’a biyata albashin wata daya ba.

Musabbabin wannan hukunci shi ne cece kucen da jama’a suka yi game da cewa an hangi minista Stella a gidan wata kawarta inda ta je cin abinci, wanda karara hakan ya saba ma dokar hana shige da fice da shugaban kasar ya sanya don kare yaduwar Coronavirus a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel