Najeriya ta karbi sawu na 2 na kayan agajin annobar Coronavirus daga China

Najeriya ta karbi sawu na 2 na kayan agajin annobar Coronavirus daga China

Gwamnatin tarayya ta karbi sawu na biyu na kayan agaji da jami’an lafiya daga kasar China, duk a kokarinta na yakar mummunan annobar nan ta coronavirus.

Jirgin Najeriya ta Air Peace ce ta dauko kayan a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu, bayan wani tashi mai dumbin tarihi da ta yi zuwa babbar birnin China wato Beijing ba tare da ta yada zango a ko ina ba.

An yi amfani da jirgin mai lamba B777-200 ER (P4 5-NBVE) wanda ya yi tafiyar awa 14 ba tare da tsayawa ba, inda ya sauka a birnin Beijing, China da misalin karfe 14:18 na ranar Talata sannan ya dawo filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a jiya Laraba, bayan tafiyar awa 15 ba tare da tsayawa ba, ya kuma sauka a kasar ne da karfe 4:25 na rana.

Najeriya ta karbi sawu na 2 na kayan again annobar Coronavirus daga China
Najeriya ta karbi sawu na 2 na kayan again annobar Coronavirus daga China
Asali: UGC

A ranar 5 ga watan Afrilu ne gwamnatin tarayya ta karbi rukunin farko na kayan asibitin daga Istanbul, kasar Turkiyya, wanda jirgin na Air Peace ne ya kwaso su.

Shugaban jirgin Air Peace, Allen Onyema ya bayyana tafiyar a matsayin mai cike da tarihi sannan ya yaba ma gwamnatin tarayya a kan jajircewarta na kare al’umman Najeriya daga mummunar annobar da ta addabi duniya.

Onyema ya kuma yi godiya ga gwamnatin tarayya a kan zabar kamfanin jirgin da ta yi domin kwaso kayayyakin daga kasashen Turkiyya da China, inda ya ce hakan babban karfafawa ne ga jiragen cikin gida da kuma inganta kasuwancin cikin gida, wanda ke sama wa matasan Najeriya aiki.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Ban san yadda aka yi Gwamna Makinde ya warke ba - Karamin Ministan Lafiya

Daga cikin kayan da jirgin Air Peace ya kwaso akwai abun gwaji tan 16, abun taimakawa numfashi wanda aka sani da ventilator, na’urar kashe kwayoyin cuta, takunkumin fuska na likitoci; magunguna, safar hannu na roba, rigar kariya, madubin ido, ma’aunin zafi da sanyin jiki da sauran kayayyakin duba marasa lafiya.

A wani rahoton kuma, mun ji cewa Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce gwamnatin tarayya za ta fara duba masu ruwa da tsaki a fannin magungunan gargajiya don yakar cutar coronavirus a kasar nan.

Ministan ya sanar da hakan ne a taron manema labarai da yayi tare da kwamitin shugaban kasar na yaki da cutar coronavirus wanda aka yi a Legas a ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng