Dakarun Sojin Najeriya sun samu karin tan-tan da manyan makamai daga China

Dakarun Sojin Najeriya sun samu karin tan-tan da manyan makamai daga China

Najeriya ta yi sayayyar sababbin makamai domin samun nasara a yakin da ta ke yi da ta’addanci. Sojoji su na sa ran wannan makamai za su taimaka wajen murkushe Makiya.

Rundunar Sojojin Najeriya ta sayo sababbin tankunan yaki daga waje. Sojojin kasar sun ce wannan ya nuna gwamnati ta na bakin kokarinta na ganin bayan duk wasu ‘Yan ta’adda.

Shugaban cibiyar da ke kula da tsare tsare da dabarun sojojin kasan Najeriya, Lafatanan Janar Lamidi Adeosun ya bayyana wannan a lokacin da ya karbi wadannan kayan yaki jiya.

Janar Lamidi Adeosun shi ne ya karbi wadannan kayan aiki a madadin Dakarun kasar. An mikawa Lamidi Adeosun makaman ne a tashar ruwan Najeriya da ke Garin Apapa a Legas.

Da ya ke jawabi a Legas, Janar Adeosun ya ce: “Mun zo ne mu shaida maraba da kayan yakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta fansowa Sojojin kasa ta hannun Ma’aikatar tsaron kasar.”

KU KARANTA: Gwamnonin da su ke da hannu wajen kafa Boko Haram a Najeriya

Dakarun Sojin Najeriya sun samu karin tan-tan da manyan makamai daga China

Soji sun samu manyan motoci da kayan yakin zamani
Source: Twitter

“An shafe tsawon lokaci ana maganar yadda za a mallaki wadannan kayan yaki, amma mun godewa Ubangiji da yanzu ya zama cewa an same su kamar yadda ku ke gani.”

Ya ce: “Za ku iya ganin irin tanadin da gwamnatin Najeriya ta ke yi ba na ganin an tara makamai kawai ba, har ma ace an shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fama da shi.”

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto cewa Sojojin Najeriya sun karbi akalla tankokin yaki da manyan makamai 17. Sojan ya ce wasu kayan yakin su na kan hanyar shigowa.

“Wadannan sababbin kaya ne, fasahar da ake yayi kenan yanzu wajen harkar motocin yaki da makaman barin wuta.” A halin yanzu sai Sojojin Najeriya sun koyi aiki da kayan.

“Daga Sin aka kawo su, akwai manyan kayan yaki, akwai kanana, haka akwai manyan bindigogi. An tura wadanda za su yi amfani da wannan kayan yaki zuwa Sin su koyo aikin.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel