Yadda Obasanjo ya biya bashin da ke kanmu duk da karancin kudin Mai - Atiku

Yadda Obasanjo ya biya bashin da ke kanmu duk da karancin kudin Mai - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fito ya yi magana game da halin da kasar ta ke ciki a yau da kuma irin tarin bashin da ke kan wuyan gwamnatin Najeriya.

Atiku Abubakar ya ce Mai gidansa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya biya duk bashin da ke kan wuyan Najeriya a lokacin da ya ke mulki duk da farashin mai bai da tsada.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa kafin annobar cutar COVID-19 ta barke a Duniya, gwamnatin Najeriya ta na kashe 42% na kudinta ne wajen biyan bashin da ake binta.

‘Dan takarar shugaban kasar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben bara, Atiku Abubakar ya ce ko da Najeriya za ta kashe kudinta kacokam wajen bunkasa tattali, ba za a kai ga ci ba.

Jaridar Vanguard ta rahoto Atiku Abubakar ya na cewa: “Ko da za mu sadaukar da 100% na kudin da mu ke samu wajen habaka tattalin arzikinmu, wadannan kudi ba za su isa ba”

KU KARANTA: Za a ragewa Ma'aikata albashi saboda a yaki COVID-19

Yadda Obasanjo ya biya bashin da ke kanmu duk da karancin kudin Mai - Atiku
Obasanjo ya biya bashin da ake bin Najeriya daga 1999 zuwa 2007
Asali: Twitter

“COVID-19 ta yi wa tatttalin arzikin Duniya mummanar barna, wannan ya bayyana a zahiri a kasashen Yamma.” Atiku ya ce ka da Najeriya ta dauka ta na da wani rigakafin cutar.

“Abin da ya sa kasashen Yammacin Duniya su ke samun yawon rahoton wadanda su ka kamu da cutar fiye da kasashe masu tasowa shi ne su na da kayan gwaji da na tattara alkaluma.”

‘Dan siyasar ya kuma nuna cewa neman ayi wa Najeriya afuwar biyan bashi a wannan marra, ba wani abin burgewa ba ne. Atiku ya ce jama’a sun kusa sanin gaskiyar halin da ake ciki.

“Wannan gaskiya ba za ta yi mana dadin ji ba, za ta girgiza mu. Da ace mun garkame tashoshin shigowa kasarmu tun wuri, da yanzu mun fi sa ran ganin karshen (wannan annoba).”

Ganin an riga an tafka kuskuren makara wajen rufe iyakokin kasar, Atiku ya ce sai dai kasar ta tari gaba. Alkaluman NCDC sun tabbatar da cewa mutane fiye da 270 sun kamu da COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel