Gwamnatin tarayya ta takawa Wike birki a kan kama direbobin jirgi

Gwamnatin tarayya ta takawa Wike birki a kan kama direbobin jirgi

Gwamnatin tarayya ta nuna fushinta a kan kama wasu matukan jirgin sama da suka kai ma’aikatan mai jahar Ribas wanda gwamnatin jahar ta sa aka yi a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu.

Ta ce kwamishinan yan sanda da kwamandan sansanin sojin sama da ke Port Harcourt za su amsa tambayoyi a kan gazawarsu.

Ministan sufirin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya yi martani a kan lamarin a Port Harcourt, inda ya ke cewa gwamnatin tarayya za ta dauki matakin da ya dace kan lamarin.

Tawagar fadar shugaban kasa kan annobar COVID-19 ta kuma bayyana rahoton cewa mambobinta na karban alawus din 500,000 a kullun a matsayin labaran karya.

Gwamnatin tarayya ta takawa Wike birki a kan kama direbobin jirgi

Gwamnatin tarayya ta takawa Wike birki a kan kama direbobin jirgi
Source: UGC

Da farko dai mun ji cewa gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, ya yi umurnin kama wasu matukan jirgin sama mai saukar ungulu su biyu kan zargin take dokar da gwamnatin jahar ta bayar, domin hana yaduwar annobar coronavirus a jahar.

Kotun majistare na Port Harcourt ta kuma tsare su a gidan yari, yayinda gwamnan ya kaddamar da cewar zai ajiye rigar kariyar da yake da shi a gefe domin shaida a kan duk wanda ya saba dokar rufe iyakar jahar.

Ya bayyana hakan ne a ofishin kwamishinan yan sandan Ribas, Mustapha Dandaura, a Port Harcourt, a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, biyo bayan kama matukan jirgin wanda Wike ya ce sun shiga jahar ba bisa ka’ida ba.

A cewar kungiyar ma’aikatan jirgi na Najeriya, matukan jirgin na muhimmin aiki ne na mai da gas, kamar yadda hukumar jirgin sama na Najeriya (NCAA) ta yarje masu.

KU KARANTA KUMA: Dakarun sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Borno, sun kashe mutum 2 sannan suka kwato motar bindiga

A wani rahoton kuma mun ji cewa, Ministan sufurin jiragen sama kuma dan kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar coronavirus, Hadi Sirika, ya sanar da jaridar Daily Trust yadda yake sauke nauyin da ke kanshi a yayin da ake fama da cutar coronavirus.

Ya sanar da wakilin jaridar Daily Trust cewa ya saka a ranshi cewa zai bautawa jama'a ne shiyasa ya karba aikin. Zai jure tare da jajircewa wajen taimakon kasarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel