Za a killace duk wanda aka kama ya shiga jihar Kaduna - Gwamnatin jiha

Za a killace duk wanda aka kama ya shiga jihar Kaduna - Gwamnatin jiha

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadin cewar yin balaguro zuwa cikin jihar ya saba wa dokokinta na kare yaduwar annobar cutar covid-19.

A wata sanarwa da gwamnan jihar ya fitar a shafinsa na tuwita, ta bayyana cewa za a dakatar da matafiya a iyakokin jihar tare da basu zabin su koma inda suka taso ko kuma su fuskanci killace wa ta tsawon kwana 14 a cibiya ta musamman.

A cewar gwamnatin jihar, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2020.

Tun a ranar 24 ga watan Maris gwamnatin jihar Kaduna ta dauki babban mataki domin kare yaduwar annobar kwayar cutar coronavirus bayan ta umarci dukkan ma'aikatanta daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida na tsawon kwanaki 30 masu zuwa.

Kazalika, gwamnatin ta umarci duk wasu 'yan kasuwa su rufe shagunansu.

Masu shagon sayar da magani da kayan abinci kadai aka yarda su bude shagunansu a jihar.

DUBA WANNAN: Jama'ar wani gida a Kaduna sun gudu sun bar gidansu bayan dan uwansu da ya dawo daga Legas ya fara zazzabi da mura

A cikin jerin wasu sakonni da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da jami'an tsaro wajen tabbatar da cewa an yi wa dokar hana jama'a da yawa taruwa a wuri guda biyayya, musamman a coci-coci, masallatai da kuma makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da ma na addini.

Gwamnan ya shawarci jama'a da su zauna a gidajensu tare da gujewa fitowa waje matukar hakan ba dole ya zama ba, saboda halin da ake ciki na fama da annobar kwayar cutar coronavirus.

Daga bisani gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci tare da rufi jihar, ba shiga, ba fita har sai yadda hali ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel