Coronavirus: Gwamnatin Sokoto ta zakulo mutane 26 da suka dawo jahar

Coronavirus: Gwamnatin Sokoto ta zakulo mutane 26 da suka dawo jahar

Rahotanni sun kawo cewa an gano mutane 29 da suka dawo jahar Sokoto daga kasashen waje da wasu yankunan kasar a kokarin da ake na hana yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar Sokoto, Muhammad Ali Inname ne ya bayyana hakan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Da yake zantawa da jaridar Caliphate Trust a jiya Talata, 7 ga watan Afrilu, kwamishinan ya bayyana cewa 11 daga cikinsu sun kammala tsarin killace kai na tsawon kwanaki 14.

Coronavirus: Gwamnatin Sokoto ta zakulo mutane 26 da suka dawo jahar

Coronavirus: Gwamnatin Sokoto ta zakulo mutane 26 da suka dawo jahar
Source: UGC

Abu mafi muhimmanci a gare mu da muke Sokoto tunda ba a samu wani da ke dauke da cutar ba shine sanya ido da kuma bibiya. Muna da wuraren bincike na tsaro da ma’aikatan lafiya guda 10 a fadin iyakokin jahar- Zamfara, Kebbi da kasar Nijar,” in ji shi.

A kan mutane da ke amfani da tsoffin hanyoyi wajen guje ma tantancewa, ya ce: “Mun sako daraktocin lafiya da hakiman garuruwa daban-daban cikin lamarin, don haka duk wanda ya shiga garuruwansu za mu samu rahoto sannan mu yi abunda ya dace.”

Ya ce domin inganta tsarin wayar da kan jama’a kan cutar a jahar, ana amfani da dabaru da dama ciki harda diban mutane da ke yiwa mutane jawabi a kauyuka.

Kwamishinan ya kuma bayyana kokarin shirya horo na musamman ga manema labarai kan COVID-19.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe wata yar kasar waje a jahar Lagas

A wani labarin kuma, wata mata yar Najeriya mai shekaru 64 a duniya Mmaete Greg ta rasu a kasar Birtaniya sakamakon kamuwa da ta yi da cutar Coronavirus, kamar yadda gwajin da aka gudanar a kanta ya tabbatar.

Mmaete wanda mazauniyar garin Landan ce ta mutu ne a ranar Litinin, 6 ga watan Maris, kamar yadda wani dan uwanta Edoamaowo Udeme ya tabbatar ma manema labaru, kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Udeme ya bayyana cewa mamaciyar tana zama ne a Birtaniya, kuma a can take aiki, inda ta kwashe sama da shekaru 40 a hukumar Yansandan birnin Landan, daga bisani ta yi ritaya da kan ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel