Gwamnatin China ta cire takunkumi a Wuhan sakamakon lafawar cutar COVID-19

Gwamnatin China ta cire takunkumi a Wuhan sakamakon lafawar cutar COVID-19

A daidai lokacin da annobar COVID-19 ta ke kara kashe Jama’a da girgiza tattalin arziki kasashe har da Najeriya. Abubuwa sun kama hanyar dawowa daidai a Garin Wuhan a kasar Sin.

Mun samu rahoto daga gidan talabijin na Al-Jazeerah dazu cewa gwamnati ta kyale mutanen Garin Wuhan da ke tsakiyar kasar Sin su fita waje a karon farko a watanni biyu da rabi.

A Ranar Laraba ne mutanen Wuhan su ka sha iskan gari tun bayan lokacin da gwamnati ta saka takunkumi. Mutanen wannan Gari sun shafe kwanaki 76 ba tare da sun leka waje ba.

A ranar da aka saki wannan takunkumi har an samu mutane fiye da 65, 000 da su ka fita a Garin. Idan ba ku manta ba wannan cuta ta COVID-19 ta fara bulla ne a Garin Wuhan a Sin.

A daidai lokacin da Sin ta ke shawo kan wannan cuta, sauran kasashen Duniya su na ta faman Wayyo Allah. Mutane kusan miliyan daya da rabi su ka kamu da wannan cuta a yanzu.

KU KARANTA: Wadanda su ka bijirewa dokar hana yawo sun shiga hannun hukuma a Najeriya

Gwamnatin China ta cire takunkumi a Wuhan sakamakon lafawar cutar COVID-19

Asibitin da Gwamnatin China ta gina a Wuhan bayan barkewar COVID-19
Source: UGC

A manyan kasashen Duniya irinsu Amurka, wannan cuta ta na cigaba da kashe Bayin Allah. Alkaluma sun tabbatar da cewa kusan mutum 400, 000 su ke dauke da cutar a Amurka.

A Ingila, Firayim Minista Boris Johnson ya na kwance a gadon asibiti. Kakakin gwamnatin Birtaniya ya tabbatar da cewa lamarin Firayim Ministan ya yi kamari har ya shiga ICU.

Alkaluman da Jami’ar Johns Hopkins ta fitar ya nuna akalla mutane 82, 000 ne wannan muguwar cuta da ta fara bayyana daga Yankin kasar Sin ta kashe a fadin kasashen Duniya.

Kamar yadda mutane su ke ta warkewa daga wannan cuta a Sin, jimilar wadanda su ka warke daga cutar a Duniya sun haura 300, 000. Wannan ya nuna akwai alamun ganin bayan cutar.

A Najeriya kuma kun ji cewa an yi rabon buhunan garin rogo da kayan abinci saboda annobar COVID-19. Talakawan Najeriya su na samun taimako daga Gwamnati a wannan lokaci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel