Allah ya jikan ‘Danuwanka Dangaladima – Bola Tinubu ga Wammako

Allah ya jikan ‘Danuwanka Dangaladima – Bola Tinubu ga Wammako

A kwanan baya ne tsohon gwamnan jihar Sokoto watau Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya rasa Kaninsa Alhaji Buba Dangaladima Wamakko

Babban Jigon jam’iyyar APC a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi maza ya aikawa tsohon gwamnan ta’aziyyar wannan rashi da ya yi.

Mai Garin Kauyen Gedawa da ke cikin karamar hukumar Wammako a jihar Sokoto, Marigayi Buba Dangaladima Wamakko, kani ne wajen Sanatan.

A wani jawabi da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fitar, ya yi wa Mamacin addu’a. babban ‘Dan siyasar ya nuna jimaminsa na rashin da Jihar ta yi.

A wasikar da ya rubuta, Bola Tinubu ya ce: “Ka karbi gaisuwata da kuma ta’aziyya game da rasuwar Kaninka, Alhaji Buba Dangaladima Wammako.”

KU KARANTA:

Allah ya jikan ‘Danuwanka Dangaladima – Bola Tinubu ga Wammako
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya rasa wani 'Danuwansa
Asali: Facebook

Alhaji Bola Tinubu ya bayyana cewa Aliyu Wammako ya rasa Kanin na sa ne ga wata rashin lafiya a Ranar Litinin ya na mai shekaru 66 a Duniya.

“Rashin ‘Danuwa na kusa irin wannan ya na da ciwo da radadi. Ina ma ace zan samu kalmomin da zan fada da za su sanyaya maka zuciya ‘Danuwana.”

Tsohon gwamnan na Legas ya ba Abokin tafiyar siyasar ta sa shawarar ya rungumi kaddara a matsayinsa na Musulmi wanda ya yi imani da Allah SWT.

“A matsayinmu na Musulmi, ya zama dole mu karbi abin da Allah ya nufa. Dole mu zama masu godiya ga Allah game da abin da ya yi a rayuwarsa.”

Bola Tinubu ya kara da cewa Alhaji Buba Dangaladima Wammako ya sha ban-ban da sauran jama’a, kuma Bayin Allah sun ga tasirinsa a rayuwarsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel