COVID-19: Gwamnatin Katsina za ta nemo wadanda su ka yi hulda da Likitan da ya mutu

COVID-19: Gwamnatin Katsina za ta nemo wadanda su ka yi hulda da Likitan da ya mutu

A Ranar Talata, 7 ga Watan Afrilu, 2020, gwamnatin Katsina ta bada sanarwar cewa cutar nan ta Coronavirus ta kashe wani Bawan Allah a jihar a makon da ya gabata.

Gwamna Aminu Bello Masari ya shaidawa ‘Yan jarida labari maras dadi na mutuwar wani Likita Dr. Aminu Yakubu wanda ya rasu a asibitin sojojin sama da ke Daura.

Wannan Bawan Allah wanda kamar yadda ku ka samu labari jiya ainihinsa Mutumin jihar Kogi ne, amma ya je Legas inda ya shafe makonni biyu a cikin kwanakin nan.

Mai girma Aminu Bello Masari ya bayyana cewa bayan dawowar wannan Likita jihar Katsina ne sai ya kamu da rashin lafiya, ya kuma kai kan shi zuwa asibiti da kansa.

Kwanaki uku da dawowar Marigayi Yakubu Katsina ne ya kwanta rashin lafiya. Ko da aka je asibitin soji, kafin a iya yin wani abu wannan Mutumi ya kwanta dama.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta sa Mutum 1 ya yi shahada a Garin Daura

COVID-19: Gwamnatin Katsina za ta nemo wadanda su ka yi hulda da Likitan da ya mutu

Za a lalubo wadanda su ka sadu da Likitan da ya mutu domin a kilace su
Source: UGC

Duk da haka Likitocin sun dauki kayan aiki, an kuma yi masa gwajin Coronavirus a Abuja, bayan kwanaki da rasuwarsa ne sakamako ya nuna ya mutu da cutar COVID-19.

A dalilin haka ne gwamnatin Katsina ta shirya yi wa mutanenta rigakafi daga wannan cuta. Likitocin ko-ta-kwana da ake da su a jihar ne za su yi wannan dawainiya.

Masari ya tabbatar da cewa wadannan Likitoci na ko-ta-kwana su na Garin Daura tun a Ranar Talata domin bin diddikin wadanda su ka hadu da Marigayin a lokacin.

“Za a bi diddikin wadanda ya yi hulda da su tun daga dawowarsa Daura har zuwa lokacin da ya rasu domin a dauki jininsu, kuma a tsaresu daga shiga cikin Jama’a.”

Gwamnan ya bayyana cewa za a tsare wadannan Bayin Allah daga shiga cikin sauran jama’a har sai zuwa lokacin da sakamakon gwajin COVID-19 da za yi masu ya fito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel