Mamaki da al'ajabi: Buhari ya bayyana na hannun daman Jonathan a matsayin dan takarar sanatan APC
An samu dimuwa a jihar Bayelsa cikin jam'iyyu biyu abokan adawar juna. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jawo wannan dimuwar tsakanin jam'iyyar APC da PDP na reshen jihar Bayelsan. Sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga Ambasada Godknows Igali ne a yayin da ya cika shekaru 60 a duniya ne ya jawo cece-kuce.
Sanannen abu ne dai idan aka ce Ambasada Igali na daga cikin jiga-jigai a jam'iyyar PDP reshen jihar Bayelsa, sannan na hannun dama a wajen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Babban mataimaki na musamman ga shugaba Buhari a kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu a ranar Litinin ya kwatanta Igali da dan takarar kujerar sanata karkashin ja'iyyar APC a zaben maye gurbi mai zuwa na jihar Bayelsa.
Ambasada Igali dai tsohon babban sakataren tarayya ne kuma ya nemi kujerar gwamnan jihar Bayelsa a karkashin jam'iyyar PDP a zaben shekarar da ta gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Hakazalika, Daily Trust ta ruwaito cewa Igali na hannun daman tsohon shugaba Jonathan ne kuma jigo a PDP ta bangaren Jonathan din.
Duk da cewa har yanzu Igali bai fito ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar PDP ba, kuma bai sanar da komawar shi APC ba.
Dan asalin karamar hukumar Ijaw ta kudu ne tare da David Lyon, wanda ya kasance dan takarar kujerar gwamnan jihar Bayelsa a zaben da ya gabata.
Karamar hukumar Ijaw kuwa yanki ne da jam'iyyar APC ta mamaye a jihar, sannan ta yi nasarar lashe zabe a yankin ko a wancan zaben da ya gabata a jihar. APC ce ta samu kaso 90 na kuri'un da aka kada a karamar hukumar na zaben gwamnoni.
KU KARANTA: COVID-19: Za mu gwada amfani da magungunan gargajiya - Ministan lafiya
Amma kuma da aka tuntubi jiga-jigan jam'iyyar APC, sun ki yin tsokaci a kan cewa ko Igali ya yi watsi da jam'iyyar ne.
Hakazalika, yayin da aka tuntubi sakataren yada labarai na jam'iyyar APC na jihar Bayelsa, Dofie Buokoribo ya ce bai san cewa Igali ya dawo jam'iyyar ba. "Bani da masaniyar cewa Ambasada Igali ya komai jam'iyyar APC. Zai fi kyau idan kuka kira fadar shugaban kasa ko sakataren jam'iyyar. Ya kamata a ce yana da masaniya," yace.
Wani mai ruwa da tsaki a siyasar jihar, Zee Debekeme ya ce jama'a daga yankin sun fara tunani a kan cancantar dan takarar ba wai jam'iyyar shi ba.
Ya kwatanta Ambasada Igali da mutum mai gogewa wanda zai iya wakiltarsu da wakilci na gari.
A yayin martani game da wannan lamarin, Igali ya ce "Shi ne shugaban kasa. Ya fi kowa sanin kowa a fadin kasar nan."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng