Yadda za mu cigaba da ciyar da dalibai duk da an rufe makarantu - Ministar jin dadi da walwala
Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda ta tsara cigaba da shirin ciyar da daliban makarantun firamare da abincin da aka noma a gida (HGSF) duk da an rufe makarantu na tsawon sati uku don dakile yaduwar cutar covid-19.
A yayin da yake gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a makon jiya, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci ministar jin dadi da walwalar jama'a, Sadiya Farouq, a kan ta bullo da wani tsari da zai tabbatar da dorewar shirin ciyar da dalibai.
Da ta ke mayar da martani a kan umarnin shugaba Buhari, ministar ta bayyana cewa za a cigaba da shirin ciyarwar a fadin kasa.
Sai dai, kalaman na Sadiya sun jawo mata suka a dandalin sada zumunta, tare da tambayar ta yaya za a cigaba da shirin yayin da aka rufe makarantu sannan aka umarci jama'a su nesanta da juna tare da hana haduwar jama'a a wuri guda.
Amma, a cikin jawabin da mataimakin darektan shirin ciyarwar, Rhoda Iliya, ya fitar ranar Talata a Abuja, Sadiya ta bayyana cewa za a koma tsarin bi gida-gida domin ciyar da daliban.
Ta ce shirin zai mayar da hankali a kan jihohin Legas, Ogun da Abuja, sannan a buda shi zuwa sauran jihohin da ke cin moriyar shirin na tsawon kwanaki 30.
"Ma'aikatar jin dadi da walwalar jama'a ta tarayya ta kammala shirye-shirye da gwamnatocin jihohi a kan bullo da sabon tsarin da zai tabbatar da cigaban shirin ciyar da dalibai da abincin da aka sarrafa a gida.
DUBA WANNAN: Rabawa talakawa shinkafa, daukan ma'aikata 774,000 da sauran matakan rage radadi 7 da FG ta dauka
"Za a bi dalibai gida-gida domin raba musu takardar shaidar karbar abinci. Takardar da za a bawa daliban za ta nuna wurin da dalibi zai karbi abincinsa, za a yi hakan ne domin gudun samun cunkuson mutane yayin rabon abincin.
"Shirin zai bawa jihohin Lagos, Ogun da Abuja fifiko sannan a fadada shi zuwa dukkan sauran jihohin da ke cin moriyar shirin inda za a kwashe kwanaki 30 ana gudanar da rabon abincin," a cewar ministar.
Kazalika, ta bayyana cewa wuraren da za a ke raba abincin, za su kasance kusa da wurin jama'a. Kuma za a tanadi ruwa mai tsafta da sinadarin tsaftace hannu a wurin domin tare da tabbatar da cewa sai dalibi ya wanke hannunsa kafin ya karbi abincin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng