Covid-19: Hukumar kwastam ta saki tireloli 247 dankare da kayan abinci da ya kai naira biliyan 3.2

Covid-19: Hukumar kwastam ta saki tireloli 247 dankare da kayan abinci da ya kai naira biliyan 3.2

Shugaban hukumar kwastam na Najeriya, Kanal Hameed Ali, ya amince da sakin manyan tireloli 247 cike da kayan tallafi, wanda farashin su ya kai naira biliyan 3.250 a kasuwa sannan harajinsu ya kai naira biliyan 2 daga dakin ajiyarsu.

A wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam, Joseph Attah, ya ce hakan na daidai da umurnin da shugaban kasa ya bayar na cewar a raba kayan da hukumar kwastam ta kwace ga al’umman kasar.

Ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon ci gaba da tsare mutane da aka yi a gida domin hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

Jawabin ya kuma bayyana cewa a martani game da radadin da ke tattare da hana mutane walwala a wasu yankunan kasar, wasu yan Najeriya sun nemi hukumar kwastam da ta raba shinkafa da sauran kayan amfani da ta kwace ga jama’a.

Covid-19: Hukumar kwastam ta saki tireloli 247 dankare da kayan abinci da ya kai naira biliyan 3.2

Covid-19: Hukumar kwastam ta saki tireloli 247 dankare da kayan abinci da ya kai naira biliyan 3.2
Source: Original

Kayayyakin sun hada da tirelar shinkafa 158 wanda aka kiyasta a tan 46,000, tirela 30 na man gyada mai lita 25 guda 36,495, da kuma jarkan man ja guda 3,428.

Sauran sun hada da tireloli 54 da ke dauke da katan din timatirin gwangwani 136,705, katan din taliya guda 2,951 da pakitin noodles 1,253, sinkin atamfofi 828 da kuma leshi 2,300.

Za a kwashi dukka kayayyakin ne a tireloli 247, domin hukumar kwastam ta ce kayan da zai dace da cin mutane kawai za a sakarwa mutane.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Gwamnatin tarayya ta raba wa talakan Najeriya garin rogo da sauran kayan abinci

A daidai lokacin kawo wannan rahoton ba a bayyana wurin da za raba kayayyakin ba tukuna.

A bangare daya mun ji cewa Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar 'yan Najeriya 774,000 a cibiyar ayyuka na musamman a kasar nan don tallafi a kan illolin annobar coronavirus.

Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne a taron manema labarai da ta gudanar don bayyana irin girgizar tattalin arziki da annobar coronavirus tayi wa kasar nan a ranar Litinin a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel