Jami'ar Tafawa Balewa ta kirkiri na'urar da ke kashe kwayar cutar covid-19

Jami'ar Tafawa Balewa ta kirkiri na'urar da ke kashe kwayar cutar covid-19

Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta kirkiri wata na'ura da za ta taimaka wajen dakile yaduwar kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

Shugaban jami'ar, Farfesa Muhammad Abdulazeez, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke magana a wurin kaddamar da na'urar wanda aka yi ranar Talata a Bauchi.

Ya bayyana cewa kirkirar na'aurar tamkar sauke nauyin da ke kan jami'ar ne a matsayinta na cibiyar bincike da kirkiro sabbin abubuwa.

Farfesa Abdulazeez ya ce yanzu haka jami'ar tana kokarin kirkirar na'urar taimakon numfashi (ventilator) da ake da bukata domin kula da lafiyar wadanda suka kamu da cutar covid-19 da ta kai mataki na 11.

"Tawagar injiniyoyi, masana kimiyya da sauran kwararru da ke jami'ar sun kirkiri na'ura kwatankwacin na'urar taimakon numfashi wacce ta ke da sauki ga kuma biyan bukata.

"Tawagar masana ta kirkiri wata na'ura ta musamman mai dauke da wani sinadari wacce za a ke amfani da ita domin rufe baki da hancin masu dauke da cutar covid-19 don kare masu duba lafiyarsu daga kamuwa daga cutar," a cewarsa.

Jami'ar Tafawa Balewa ta kirkiri na'urar da ke kashe kwayar cutar covid-19
Jami'ar Tafawa Balewa da ke Bauchi
Asali: UGC

Shugaban tawagar kwararrun, Faisal Bala, ya ce na'urar da suka kirkira tana sarrafa kanta tare da yi wa duk wani mai shiga ko fita daga daki feshin sinadarin da zai kashe kwayar cutar.

Ya bayyana cewa suna aiki hannu da hannu da sashen karatun likitanci na jami'ar domin samar da wasu sauran na'urorin da za a iya amfani da su wajen dakile yaduwar covid-19.

DUBA WANNAN: Covid-19: Rukunin farko na kayan duba lafiya da FG ta sayo daga Turkiyya sun iso Najeriya

A cewar Farfesa Abdulazeez, jami'ar ta shiga kirkirar wadannan na'urori ne saboda kudin da ake kashewa da kuma wahalar da ake sha kafin sayo su domin a duba lafiyar wadanda suka kamu da covid-19, zazzabin Lassa da sauran cututtuka masu yaduwa.

"Jami'ar ta yanke shawarar zurfafa bincike, kuma ga shi a karshe mun yi nasarar samar da kwatankwacin na'urorin," a cewarsa.

Kazalika, ya bayyana karancin kudi a matsayin babban kalubalen da samar da na'urorin da yawa ke fuskanta.

Farfesa Abdulazeez ya yi kira ga gwamnatoci a kowanne mataki da su gaggauta tuntubar sashen karatun injiniya (Mechatronics) domin a kera musu adadin na'urorin da suke bukata.

Ya kara da cewa jami'ar ta kirkiro wadannan na'urori ne ba don ta na son samun riba ba, sai don bayar da gudunmawarta a yaki da annobar cutar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng