Coronavirus: CBN ya gargadi mutane a kan yan damfara

Coronavirus: CBN ya gargadi mutane a kan yan damfara

Rahotanni sun kawo cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya gargadi mutane a kan wasu miyagu da ke amfani da halin da ake ciki na annobar coronavirus wajen damfarar mutane.

A bisa ga wata sanarwa daga kakakin CBN, Isaac Okorafor, ya bayyana cewa mazambatar na yanar gizo na amfani da damar annobar da ake ciki wajen damfarar al’umman kasar da sace bayanansu wajen yi musu kutse a kwamfuta ko wayoyin salularsu ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa daban-daban.”

Babban bankin ya ce yan damfarar na amfani da hanyoyin sadarwa wajen aika sakon imel ga mutane, inda suke ikirarin cewa daga hukumar lafiya ta duniya ko cibiyar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ne, sannan sai su nemi mutane su danna mashigin shafin, amma da zarar mutum ya yi hakan, sai su mayar dashi shafin da za su damfare shi.

Coronavirus: CBN ya gargadi mutane a kan yan damfara

Coronavirus: CBN ya gargadi mutane a kan yan damfara
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Covid19: Yadda mutane suka yi wawaso wurin rabon tallafin kayan abinci a Kaduna

Ya ci gaba da cewa babban burin bankin shi ne wayar wa da mutane da ke hulda da shi kai game da wannan mummunar dabi’a don kada su bari a damfare su.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kungiya mai zaman kanta mai suna SERAP ta roki gwamnatin tarayyar Najeriya da babban bankin kasar na CBN su fadawa jama’a yadda ake kashe gudumuwar da ake tarawa.

Kungiyar SERAP ta na so gwamnatin Najeriya ta yi bayani dalla-dallar game da inda gudumuwar da Bayin Allah da Attajirai su ka tara domin yaki da annobar COVID-19, su ke shiga.

SERAP mai bin diddiki ta na so a bayyana sunayen wadanda aka ba kudi a matsayin tallafi na annobar da aka shiga. Wannan ne zai sa jama’a su san inda dukiyar kasar ta ke tafiya.

Wannan kungiya ta SERAP ta na son samun cikakken bayani game da wadanda aka ce an rabawa kayan abinci a Legas da Ogun inda aka hana fita saboda barkewar COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel