Asibitocin mu sun cika babu inda zamu saka ku - Martanin kasar Amurka ga mutanenta na Najeriya da suke son komawa gida

Asibitocin mu sun cika babu inda zamu saka ku - Martanin kasar Amurka ga mutanenta na Najeriya da suke son komawa gida

- Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da 'yan kasarta cewa su tanadi kudin tafiyarsu da na asibiti matukar za su koma Amurka

- Kamar yadda takardar da ta fito daga ofishin jakadancin kasar a Najeriya ya bayyana, za a kwashe 'yan kasar Amurkan don komawa gida

- Kamar yadda takardar ta bayyana, duk mai komawa ya nema wajen zama don duk otal a rufe suke kuma suna ci gaba da rufewa

Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da 'yan kasarta da ke son komawa daga Najeriya a kan halin da cibiyar lafiyar kasar ke ciki.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa, a takardar da ta fita a ranar Lahadi, 5 ga watan Afirilu, ofishin jakadancin kasar Amurkan da ke Najeriya ya ce asibitocin kasar na da rinjaye.

Bayan wannan sanarwar ga 'yan kasar Amurkan, an bayyana musu cewa dole ne su dau nauyin biyan kudin tafiyarsu zuwa kasar. Ofishin jakadancin ya kara bayyana cewa babu inshorar lafiya a halin yanzu sakamakon yanayin cibiyoyin lafiyar.

Asibitocin mu sun cika babu inda zamu saka ku - Martanin kasar Amurka ga mutanenta na Najeriya da suke son komawa gida

Asibitocin mu sun cika babu inda zamu saka ku - Martanin kasar Amurka ga mutanenta na Najeriya da suke son komawa gida
Source: Instagram

Takardar ta ce: "Dole ne fasinjoji su saka hannu a kan yarjejeniyar kuma dole ne su biya kudin jirginsu. Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja tare da jakaden kasar a Najeriya za su so wadanda za su koma Amurka su san wasu sharudda,"

"Da kan kowa zai biya kudin jirgi har zuwa kasar Amurkan. Dukkan fasinjoji dole su sa hannu a kan takardar yarjejeniya sannan su biya kudin jirgi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu

"Hakazalika, matafiya dole ne su biya kudin mota har gidansu a Amurka da kuma kudin dawowa Najeriya idan sun so. Kudin komawar zai kama daga $1,300 zuwa $2,400 na duk mutum daya.

"Tsarin cibiyoyin lafiya na kasar Amurka yanzu sun sauya. Idan akwai bukatar zuwa asibiti, za a biya kudi ne don yanzu babu inshorar lafiya.

"Otal a Amurka suna ta rufewa. Idan za ku koma Amurka, ku tabbatar da cewa kuna da wurin zama kafin ku tafi. A wannan lokacin, filayen jiragen sama sun hana jiragen kudi sauka da tashi. Idan kuka tafi Amurka, babu yuwuwar za ku dawo Najeriya har sai gwamnati ta bude filayen jiragen saman."

A ranar Litinin, 6 ga watan Afirilu, kasar Amurka ta tabbatar da cewa mutane 334,851 ne suka suka kamu da cutar coronavirus. Mutane 9,620 ne suka mutu inda mutane 17,977 suka warke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel