Majalisa ta tsawaita hutunta domin bin dokar hana zirga-zirga

Majalisa ta tsawaita hutunta domin bin dokar hana zirga-zirga

Majalisar dattawan Najeriya ta tsawaita hutunta domin bin umurnin hana zirga-zirga da gwamnatin tarayya ta yi a kokarinta na hana yaduwar cutar Covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus.

Covid-19 ta kasance mummunar cuta ta numfashi. Ta harbi mutane sama da miliyan daya a fadin duniya yayinda ta haddasa mutuwar sama da mutane 60,000.

Kakakin majalisar dattawa, Godiya Akwashiki ya tabbatar da tsawaita hutun majalisar a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, jaridar Premium Times ta ruwaito.

A cewarsa, an yanke wannan shawara ne domin bin umurnin rufe harkoki da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na tsawon kwanaki 14.

Majalisa ta tsawaita hutunta domin bin dokar hana zirga-zirga
Majalisa ta tsawaita hutunta domin bin dokar hana zirga-zirga
Asali: UGC

“A’a ba zamu dawo zama ba a yau, saboda dokar hana walwala,” in ji shi.

Da farko dai, Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Abdullahi Yahaya, ya tabbatar wa da manema labarai cewa: “majalisar dattawan za ta bi umurnin Shugaban kasa.”

Sai dai, a lokacin da aka tambayi ko majalisar dattawan za ta yi zaman gaggawa domin duba bukatar Shugaban kasa na ranto naira biliyan 500, Mista Akwashiki ya ce ba zai iya cewa komai kan haka ba domin yan majalisar ba su riga sun amince kan haka ba.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Buhari ya amince da daukar ma'aikata 774,000

A wani labari na daban, Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya koka da yadda labaran bogi ke yaduwa a kan gwamnatin tarayya wanda hakan ke janye hankalinsu daga yakar muguwar cutar coronavirus a kasar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Mohammed ya jajanta cewa akwai mutanen da ke dauke hankalin mulkin shugaba Buhari daga yakar muguwar cutar coronavirus, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

A yayin da yake bada misali, ministan ya ce: "Daya daga cikin labaran bogin kwanakin nan shine wanda aka ce babu yunwa a kasar nan kuma gwamnatin tarayya ta fitar da naira biliyan dari ga 'yan Najeriya. Labarin bogi ne kuma ni ban sanar da hakan ba."

Duk da cewa ministan bai fitar da sunaye ba, amma ya ce masu yada labaran bogin basu denawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel