Attajirin kasar China ya bawa Najeriya tallafin na'urar taimakon numfashi guda 500

Attajirin kasar China ya bawa Najeriya tallafin na'urar taimakon numfashi guda 500

Biloniya a kasar China, Jack Ma, ya sake aiko da karin wasu kayan duba lafiya da suka hada da na'urar taimakon numfashi 500 zuwa kasashen Afrika 54 domin su yaki cutar covid-19.

Ma, attajirin dan kasuwa, ya sanar da hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Ya bayyana cewa sauran kayan da ya bayar da tallafinsu sun hada da kayan sakawar ma'aikatan lafiya 200,000, takunkumin rufe fuska 200,000, na'urar sanin sanyi ko zafin jiki 2,000, safar hannu 500,000 da sauransu.

A ranar 25 ga watan Maris ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta fara jigilar tallafin kayan kiwon lafiya da gidauniyar wani attajiri dan kasar China, Jack Ma Foundation, ta bawa Najeriya domin yakar annobar cutar coronavirus.

NAF ta fara jigilar kayan tallafin ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Murtala Mohammed International Airport (MMIA), da ke jihar Legas zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Nnamdi Azikiwe International Airport (NMIA), da ke Abuja a ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Kayan tallafin sun hada da wasu akwatuna 107 da ke cike da kayan duba lafiya da suka hada da kayan tiyata, kayan gano kwayar cutar corona, kayan ma'aikatan asibiti da ke duba marasa lafiya da sauransu.

Attajirin kasar China ya bawa Najeriya tallafin na'urar taimakon numfashi guda 500

Na'urar taimakon numfashi guda 500
Source: Twitter

Bayan isowar kayan tallafin Abuja, NAF ta damka su a hannu wakilan ma'aikatar lafiya a karkashin jagorancin babban sakataren ma'aikatar, Abdulazeez Mashi Abdullahi, a ranar Laraba, 25 ga watan Maris.

Da yake magana da manema labarai jim kadan baya karbar kayan tallafin, Alhaji Abdullahi ya mika godiya ta musamman ga shugaban rundunar NAF, Air Marshal Sadique Abubakar, bisa jigilar kayan a kan lokaci zuwa Abuja.

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta fara jigilar tallafin kayan kiwon lafiya da gidauniyar wani attajiri dan kasar China, Jack Ma Foundation, ta bawa Najeriya domin yakar annobar cutar coronavirus.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano

NAF ta fara jigilar kayan tallafin ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Murtala Mohammed International Airport (MMIA), da ke jihar Legas zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Nnamdi Azikiwe International Airport (NMIA), da ke Abuja a ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Kayan tallafin sun hada da wasu akwatuna 107 da ke cike da kayan duba lafiya, kayan tiyata, kayan gano kwayar cutar corona, kayan ma'aikatan da ke duba marasa lafiya da sauransu.

Bayan isowar kayan tallafin Abuja, NAF ta damka su a hannu wakilan ma'aikatar lafiya a karkashin jagorancin babban sakataren ma'aikatar, Abdulazeez Mashi Abdullahi, a ranar Laraba, 25 ga watan Maris.

Da yake magana da manema labarai jim kadan baya karbar kayan tallafin, Alhaji Abdullahi ya mika godiya ta musamman ga shugaban rundunar NAF, Air Marshal Sadique Abubakar, bisa jigilar kayan a kan lokaci zuwa Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel