Dokar hana fita: Wani dan sanda ya kashe ma’aikacin gidan mai

Dokar hana fita: Wani dan sanda ya kashe ma’aikacin gidan mai

An zargi wani jami’in dan sanda a jahar Abia da kashe wani ma’aikacin gidan mai a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu. Lamarin ya afku ne a sabuwar hanyar Umuahia a karamar hukumar Obingwa.

Dan sandan, Stanley Azu, na aiki a karkashin ofishin yan sanda na Azumini a karamar hukumar Ukwa ta gabas a jahar Abia.

An tattaro cewa ya yi kokarin tsayar da wata mota da ta saba dokar hana fita sakamakon annobar Coronavirus, amma sai direban ya yi watsi da umurnin.

Dokar hana fita: Wani dan sanda ya kashe ma’aikacin gidan mai
Dokar hana fita: Wani dan sanda ya kashe ma’aikacin gidan mai
Asali: Facebook

Mazauna yankin sun ce sufeton dan sandan ya fatattaki direban sannan ya bude masa wuta.

Harsashin ya samu Chibuisi, wanda ke wajen kasuwancinsa.

An tattaro cewa an sanar da mutuwar Chubuisi a asibitin koyarwa na jahar Abia inda aka yi gaggawan kai shi bayan afkuwar lamarin.

Kafin mutuwarsa, Chibuisi ya kasance ma’aikaci a gidan man Greenmac Energy Ltd malakar surukinsa.

Kwamishinan yan sandan jahar, Ene Okon, ya tabbatar da lamarin,

Ya ce an kama jami’in sannan cewa an kai shi sashin binciken masu laifi kan lamarin.

Mista Okon ya ce rundunar yan sandan bata yarda da irin wannan aiki ba.

KU KARANTA KUMA: COVID-19 ta fara yaduwa tsakanin junan ‘Yan Najeriya – Minista

A wani rahoton kuma, mun ji cewa akalla mutane biyar ne suka mutu a ranar Litinin sakamakon wani rikici da ya kaure tsakanin matasan unguwar Tirkania dake cikin sabon garin Nassarawa, a karamar hukumar Chikun da jami’an rundunar Yansandan jahar.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito rikicin ya kaure ne a daidai lokacin da Yansandan suka yi kokarin dabbaka umarnin gwamnatin jahar Kaduna na hana zirga zirga da shige da fice a jahar domin kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Majiyar ta ruwaito cewa wasu yan kasuwa ne suka taru a wani shingen wucin gadi dake unguwar Tirkania suna sayar da hajojinsu sakamakon garkame kasuwar Monday da gwamnatin jahar ta yi saboda dokar ta baci.

Da fari dai matasan sa kai na Civilian JTF ne suka fara kokarin fatattakar yan kasuwan daga inda suke cinikayyar, amma matasan unguwar suka nuna musu tirjiya, har ma suka nemi su fi karfin yan Civilina JTF din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng