Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu

Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu

- Shugabannin cibiyoyin lafiya na kasar Koriya ta Kudu sun bayyana cewa akwai yuwuwar kwayar cutar coronavirus na iya tashi daga baya idan an warke

- Shugabannin kuwa sun yi wannan hasashen ne bayan wasu mutane 51 sun kara kamuwa da cutar bayan warkewarsu

- Amma kuma kwararru sun bayyana cewa hakan ba za ta yuwu ba don da aka gwada a birai hakan bata faru ba

Shugabannin cibiyoyin lafiya na kasar Koriya ta Kudu sun bayyana cewa kwayar cutar coronavirus na iya suma a jikin dan Adam sannan ta sake tashi bayan kwanaki. Sun sanar da hakan ne kuwa bayan mutane 51 da suka warke daga cutar sun sake bayyana da ita bayan kwanaki kadan da aka sallamesu daga asibiti.

Majinyatan, wadanda suke daga yankin Daegu, an killace su ne bayan an gano suna dauke da cutar a karo na biyu, kamar yadda shagin Linda Ikeji ya wallafa.

Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu

Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu
Source: UGC

Kamar yadda cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta kasar Koriya din ta bayyana, majinyatan dai sun fito ne daga sashin kasar da cutar ta fi yi wa illa. An kuma killace su ne kuma ana zargin kwayar cutar ta sake tashi ne bayan an kasheta daga jikinsu.

Kamar yadda KCDC ta bayyana, har yanzu dai ba a gano dalilin da yasa kwayar cutar ke sake tashi ba bayan an kasheta a jikin dan Adam. Amma kuma kwararru a fannin kiwon lafiya sun sanar da cewa babu tabbacin kwayar cutar za ta iya yin hakan bayan binciken da aka gabatar a jikin biri.

KU KARANTA: An garkame dan takarar gwamnan jihar Legas saboda ya karya dokar da gwamnati ta sanya ta hana fita

Paul Hunter farfesa ne a fannin karantar kwayoyin cutuka masu yaduwa a jami'ar Gabas din Anglia. Ya sanar da jaridar MailOnline cewa: "Zan iya yarda cewa sun sake kamuwa da cutar amma bana tunanin kwayoyin cutar ne suka sake tashi a jikinsu. Akwai yuwuwar cewa gwajin karshen ba gaskiya bane."

Farfesa Mark Harris na jami'ar Leeds ya ce: "Rahoton cewa wadanda suka rabu da cutar sun sake kamuwa da cutar abun damuwa ne. Zai yuwu dai sun sake samun cutar ne ba wai tashi kwayoyin cutar suka yi ba. Akwai yuwuwar kuma ba su warke sarai bane daga cutar."

Farfesa Rowland Kao na jami'ar Edinburgh ya ce: "Wannan lamarin zai yuwu ba zai iya faruwa ba. Illa kadan zai iya kawowa ga barkewar annobar a duniya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel