An yi rikici tsakanin Yansanda da matasa a Kaduna, mutane 5 sun mutu

An yi rikici tsakanin Yansanda da matasa a Kaduna, mutane 5 sun mutu

Akalla mutane biyar ne suka mutu a ranar Litinin sakamakon wani rikici da ya kaure tsakanin matasan unguwar Tirkania dake cikin sabon garin Nassarawa, a karamar hukumar Chikun da jami’an rundunar Yansandan jahar.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito rikicin ya kaure ne a daidai lokacin da Yansandan suka yi kokarin dabbaka umarnin gwamnatin jahar Kaduna na hana zirga zirga da shige da fice a jahar domin kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

KU KARANTA: Habbatissaudah da zuma ne suka warkar da ni daga Coronavirus – Gwamna Makinde

An yi rikici tsakanin Yansanda da matasa a Kaduna, mutane 5 sun mutu
An yi rikici tsakanin Yansanda da matasa a Kaduna, mutane 5 sun mutu
Asali: Facebook

Majiyar ta ruwaito cewa wasu yan kasuwa ne suka taru a wani shingen wucin gadi dake unguwar Tirkania suna sayar da hajojinsu sakamakon garkame kasuwar Monday da gwamnatin jahar ta yi saboda dokar ta baci.

Da fari dai matasan sa kai na Civilian JTF ne suka fara kokarin fatattakar yan kasuwan daga inda suke cinikayyar, amma matasan unguwar suka nuna musu tirjiya, har ma suka nemi su fi karfin yan Civilina JTF din.

Wannan ne tasa aka turo karin jami’an Yansanda daga ofishin Yansanda na Kakuri, inda zuwan su ke da wuya suka bude ma matasan wuta, nan take mutane biyar suka fadi matattu, yayin da wasu da dama suka samu munanan rauni.

Amma da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, Mohamamd Jalige game da aukuwar lamarin, sai ya ce ba shi da masaniya saboda bai samu wani rahoto dangane da rikicin ba.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Taraba ta sanar da kama wata mata mai suna Mary Yakubu tare da wasu kananan yara guda 27 da ta sato su daga sassa daban daban na jahar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, David Misal ne ya sanar da kama matar a ranar Litinin, inda ya ce sun ceto yara 60 daga hannunta zuwa yanzu.

Misal ya ce sun ceto yaran ne daga hannun Mary a ranar Lahadi a tashar Takalma dake karamar hukumar Gassola na jahar Taraba, daga cikin yaran dake hannunta akwai mata 13 da maza 14.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel